Yan Sanda Za Su Buga Wasan Kwallo Da Tubabbun 'Yan Daba a Kano

Yan Sanda Za Su Buga Wasan Kwallo Da Tubabbun 'Yan Daba a Kano

  • Hukumar yan sandan Kano ta ce zata shirya wasan kwallon cikin gida tsakanin jami'anta da tubabbun 'yan daba
  • CP Muhammed Usaini Gumel ne ya tabbatar da haka yayin nuna mutane 108 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban lokacin babbar sallah
  • Ya bayyana cewa hankalinsu ya koma kan sabon salon da yan daba suka bullo da shi a kwaryar birnin Kano kuma tuni suka fara ɗaukar matakai

Kano state - Hukumar 'yan sanda reshen jihar Kano ta ce zata shirya wasan kwallo na musamman tsakanin jami'anta da kuma tubabbun 'yan daba.

Kwamishinan yan sandan Kano, Muhammed Usaini Gumel, shi ne ya tabbatar da haka inda ya ce zasu yi wasan ne domin tabbatar da cewa 'yan daban sun yi tubar gaskiya.

Yan sanda na kokarin kawo karshen ayyukan 'yan daba a Kano.
Yan Sanda Zasu Buga Wasan Kwallo da Tubabbun 'Yan Daba a Kano Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamishinan ya faɗi haka ne yayin nuna mutum 108 da 'yan sanda suka kama kan zargi daban-daban lokacin shagulgulan babbar Sallah.

Kara karanta wannan

Bidiyon Dala: Gwamnati Ta Janye Ƙarar da ta Haramtawa EFCC Binciken Ganduje

A kalamansa, CP Gumel ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Zamu bi hanyoyi daban-dabn domin sauya rayuwar 'yan daba su zama mutanen kirki. Zamu shirya gasar ƙwallo, zamu taka leda mu kara da, zamu buga wasan cikin gida."
"A yanzu hankalin mu ya koma kan sabbin hanyoyin da 'yan daba suka bullo da su musamman a cikin kwaryar birnin Kano, ba zamu yi ƙasa a guiwa ba, mun tsara dabaru da fasahar shawo kan aikata manyan laifuka a sassan Kano."

Wane mataki 'yan sanda ke ɗauka a Kano?

Bayan haka, kwamishinan 'yan sandan ya bayyana sunayen wasu manyan 'yan daba a sassa daban daban, kuma ya umrci su miƙa kansu hannun 'yan sanda tun da arziki.

Sunayen da ya ambata sun haɗa da, Messi na Kan Tudun Dala; Dan Boss daga Dala Makabarta; Ado Runto a Tudun Fulani; Baffa Makashi a Mazaunar Tanko Quarters da Kamilu Duna a Adakawa Quarters.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Kwanta da Ita, Wani Ɗan Kasuwa Ya Saki Hotuna 50 Na Tsiraicin Wata Mata, Ya Shiga Matsala

Ya ce dukkan waɗanda nan da wasu da ya bayyana sunayensu, su hanzarta mika kansu idan ba haka ba, hukumar zata ayyana nemansu ruwa a jallo.

'Yan Fashi Sun Kai Farmaki Fadar Mai Martaba Sarkin Minna, Sun Harbi Mutum 2

A wani labarin na daban kuma 'Yan fashi sun aikata ta'adi ido na ganin ido a fadar mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, ranar Talata.

Yan fashi da makamin sun kutsa kai fadar kuma sun harbi dogarai biyu a harin wanda ake tsammanin sun biyo ɗaya daga cikin hadiman fadarɓne tun da farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262