Abba Kyari Ba Zai Tafi Gida Ba Duk Ba Kotu Ta Bada Belinsa, Alkali Ya Yi Karin Haske

Abba Kyari Ba Zai Tafi Gida Ba Duk Ba Kotu Ta Bada Belinsa, Alkali Ya Yi Karin Haske

  • Babbar kotun tarayya ta bayar da Belin dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sanda Abba Kyari
  • An bayyana cewa duk da belin N50m da aka ba Abba Kyari, har yanzu ba za a iya sakinsa daga gidan yari ba
  • Mai shari'a James Omotosho, ya bayyana cewa za a saki Abban ne kawai in an ƙarƙare ɗayar shari'arsa da NDLEA

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta, bayar da belin Abba Kyari a kan kuɗi naira miliyan 50.

Sai dai an bayyana cewa ba za a saki dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sandan ba duk da wannan beli nasa da aka bayar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An bayyana abinda zai hana a saki Abba Kyari
Alkali ya yi karin haske kan belin da aka bai wa Abba Kyari. Hoto: Hamza N Dantani
Asali: Facebook

Kotu ta ba da belin Abba Kyari kan tuhume-tuhumen da ake masa

Abba Kyari, wanda ke fuskantar tuhuma kan ƙin bayyana kadarorinsa tare da ‘yan uwansa, ya samu beli a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Ganduje Ya Bayyana Ainihin Dalilin Da Ya Sa Aka Tado Da Maganar 'Bidiyon Dala'

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta gurfanar da DCP Kyari da ‘yan uwansa Mohammed Baba da Ali a gaban kotu.

Hukumar ta cike tuhume-tuhume 24 kan Abba sakamakon ƙin bayyana wasu kadarori da ake zargin suna da alaka da shi.

A kwanakin baya ne aka ba da belin ‘yan’uwan Kyari da ake zargi da karɓar kuɗaɗe daga ƙasurgumin ɗan damfara, Ramoni Abbas da aka fi sani da Hushpuppi, wanda aka alaƙanta da Abban.

A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a James Omotosho ya bayar da belin Kyari a kan kuɗi N50m da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.

Mai shari’a Omotosho ya ƙara da cewa, dole ne waɗanda za su tsaya masa su mallaki kadarar da ta kai ta N25m a inda kotun ke da iko.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bada Belin Abba Kyari Bayan Shafe Wata 18 A Gidan Gyaran Hali

Abba Kyari zai ci gaba da zama a tsare kan wani laifin na daban

Alƙalin ya bayyana cewa sakin Kyari ya dogara ne ga hukuncin da aka yanke kan tuhumar da ake masa da wasu mutane huɗu kan laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi kamar yadda The Sun ta wallafa.

Mai shari’a Omotosho ya ce zai sanya hannu ne kawai kan takardar sakinsa idan an kammala sauran shari’o’in da ake yi na sauran laifukan, ko kuma in an bayar da belinsa a waɗancan shari’o’in.

An naɗa mace ta farko a matsayin alƙalin alƙalan Kano

Legit.ng ta kawo muku wani rahoto a baya kan labarin mace ta farko da ta zama alƙalin alƙalai a jihar Kano.

Majalisar Dokokin jihar Kano a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli ta tabbatar da naɗin Dije Abokin a matsayin alƙalin alƙalan jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

iiq_pixel