Matashi Ya Yi Wa Matarsa Ruwan Bandir-Bandir Na Yan N20, Matar Ta Kama Kafafunsa

Matashi Ya Yi Wa Matarsa Ruwan Bandir-Bandir Na Yan N20, Matar Ta Kama Kafafunsa

  • Bidiyon wani mutum yana likawa wata matashiya da ta durkusa a gabansa bandir-bandir na yan N20 ya yadu a TikTok
  • Ga dukkan alamu, mutumin na nuna godiya ne ga matarsa wacce ke goye da yaro a bayanta
  • Matar ta cika da farin ciki ta yadda har ta rungume mutumin wanda ya ci gaba da yi mata yayyafin kudi

Wani bidiyo da ya yadu a dandalin TikTok ya nuno wani magidanci yana yi wa matarsa yayyafin kudi bandir-bandir na yan N20 yayin da ita kuma ta durkusa a gabansa.

Mutumin ya nuna kamar yana nuna godiyarsa ga matar tasa ce wacce ke goye da kyakkyawan yaro a bayanta inda shi kuma ya ci gaba da yi mata yayyafin kudi.

Magidanci yana likawa matarsa kudi
Matashi Ya Yi Wa Matarsa Ruwan Bandir-Bandir Na Yan N20, Matar Ta Kama Kafafunsa Hoto: @garebillion
Asali: TikTok

Matashi ya likawa matarsa kudi yan N20

Matar ta cika da farin cikin wannan karamci da sahibin nata ya nuna mata yayin da ta rungume shi inda shi kuma ya ci gaba da yi mata ruwan kudi.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Koka Yayin da Mai Gidansu Ke Nemanta, Ya Ce Ba Za Ta Dunga Biyan Kudin Haya Ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka kalli bidiyon sun sha dariya inda suka ce duk tunaninsu daloli ne.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a kan bidiyon matashi da ke likawa matarsa bandir din N20

@Davidportal ya yi martani:

"Waye kuma ya zata dala ne."

@Teemah t ce:

"Shi da ya kashe naira shine zai kashe dubbai, akalla dai ya bayar da abun da yake da shi, yayin da wasu basa nuna damuwa ga matansu."

@perrywhite ta rubuta:

"Akalla ya yi kokari, ku dunga yabawa duk kankantar abu."

@sherrywhite ta yi martani:

"Idan ya samu fiye da ahaka, zai yi fiye da haka."

@Sugarplum:

"Murmusa idan ya samu fiye da haka zai yi sama da ahaka."

@user4748848584 ma ya yi martani:

"Ba dukka hannu ne daya ba akalla dai suna farin ciki."

Kara karanta wannan

Garin Kallon Ruwa: Budurwa Ta Koka Yayin da Mai Sonta Ya Koma Ga Wata Bayan Ta Ja Mai Aji

Matashiya ta koka, ta ce mai gidansu na nemanta, ya yi alkawarin yafe mata kudin haya

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta garzaya soshiyal midiya domin neman shawarar mutane kan bukatar da mai gidan da take haya ya bijiro mata da shi.

A cewar matarshiyar, mutumin ya nemi su kulla alaka a tsakaninsu inda shi kuma zai yafe mata biyan kudin haya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng