Gwamnatin Imo Ta Musanta Raɗe-Radin Yan Bindiga Sun Kai Hari Sakatariyar Jiha

Gwamnatin Imo Ta Musanta Raɗe-Radin Yan Bindiga Sun Kai Hari Sakatariyar Jiha

  • Gwamnatin jihar Imo ta karyata labarin da ke yawo cewa 'yan bindiga sun kai farmaki gidan gwamnatin jiha a Owerri
  • A wata sanarwa, gwamnatin ta ce yan sanda ne suka zo kama wani mai hannu a laifin da ya shafi ta'addanci kuma su ne suka yi harbin gargaɗi
  • Ta buƙaci mazuana Imo su kwantar da hankulansa zata ci gaba da yin duk abin ya dace don tabbatar da zaman lafiya

Imo state - Gwamnatin jihar Imo ta musanta rahoton da ake yaɗawa cewa 'yan bindigan da ba'a sani ba sun kai farmaki gidan gwamnatin jihar da ke Owerri.

Gwamnatin ta musanta raɗe-raɗin kai harin a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamna Hope Uzodinma na Imo, Oguwike Nwachuku, ya raba wa manema labarai.

Gwamnatin Imo ta musanta kai hari babbar Sakatariyar jiha.
Gwamnatin Imo Ta Musanta Raɗe-Radin Yan Bindiga Sun Kai Hari Sakatariyar Jiha Hoto: Imo State Media Office
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna cewa tuni aka fara yaɗa jita-jitar cewa yan bindiga sun kai hari gidan gwamnatin Imo da ke kan titin Owerri-Patakwal a Owerri, babban birnin jiha bayan jin karar harbe-harbe.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Mamakon Ruwan Sama Ya Yi Awon Gaba Da Mutane 2 a Birnin Katsina

Amma kakakin gwamna ya musanta ikirarin da cewa 'yan sanda ne suka yi harbe-harben yayin da suka je Sakatariyar jiha domin kama wani da ake zargi da aikata babban laifi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A rahoton da jaridar Vanguard ta tattaro, Sanarwan ta ce:

"An ja hankalin gwamnatin Imo bisa wani labari da ke yawo cewa 'yan bindiga sun kai farmaki gidan gwamnatin jiha da ke kan titin Patakwal da safiyar nan, inda suka bude wuta, ma'aikata suka watse domin tsire da rayuwarsu."
"Wannan ba gaskiya bane, ba bu wani abu da ya faru mai alaƙa da 'yan bindigan da ba'a sani ba. Abinda ya faru 'yan sanda ne suka biyo wani mutumi da ake zargi da hannu a Kes din ya shafi ta'addanci."
"Sun biyo shi har cikin gidan gwamnati kuma a yunkurin damƙe shi ne 'yan sanda suka yi harbin gargaɗi. Don haka muna kira ga al'umma su yi watsi da labarin kai farmaki domin ba bu wani abu mai kama da haka."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Fadar Sarkin Minna Wuta Kuma Yana Ciki, Sun Tafka Ta'adi

Daga karshe, gwamnatin ta ƙara tabbatar wa mutanen jihar Imo cewa zata yi duk mai yuwuwa wajen kare rayuka da dukiyoyinsu, Guardian ta tattaro.

Yan Fashi Sun Kai Farmaki Fadar Mai Martaba Sarkin Minna, Sun Harbi Mutum 2

A wani labarin na daban kuma Wasu 'yan fashi ɗauke da bindigu sun kai farmaki fadar mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, da yammacin ranar Talata.

Bayanai sun nuna cewa Sarki na cikin fada sa'ilin da maharan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin tsorata mutane, daga bisani suka yi awon gaba da maƙudan kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262