Yan Sanda Sun Fara Farautar Mutumin Da Ya Yada Hotunan Tsiraincin Bazawara a Legas
- 'Yan sanda sun baza komar farautar wani ɗan kasuwa a jihar Legas bisa zargin wallafa Hotunan tsiraicin wata mata
- Bayanai sun nuna mutumin ya haɗu da matar a kafar sada zumunta, suka haɗu a Otal har ya kwanta da ita kuma ya ɗauki Hotuna
- Hukumar yan sanda ta nemi ya miƙa kansa ya tabbatar ba shi laifi idan kuma ya ƙi doka zata damƙo shi
Lagos - Hukumar 'yan sandan jihar Legas ta buƙaci wani ɗan kasuwa, Amarah Kennedy, ya hanzarta miƙa kansa ya yi bayanin da zai gamsar cewa ba shi da hannu a yaɗa Hotunan tsiraici.
Hukumar 'yan sanda ta yi kira ga ɗan kasuwan ya gaggauta zuwa ya yi bayani kan zargin da ake masa na yaɗa Hotunan tsiraicin wata bazawara a soshiyal midiya.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana haka a sahihin shafinsa na Tuwita ranar Laraba.
Ya ce kwamishinan 'yan sanda a jihar Legas, CP Idowu Owohunwa, ya gana da matar da lamarin ya shafa a Ofishinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"CP ya tabbatarwa matar cewa za'a mata adalci kuma ya umarci sashin likitocin hukumar 'yan sanda su ba ta duk tallafin da ya dace."
"Shi kuma wanda ake zargi, muna ba shi shawarin ya miƙa kansa ya yi bayanin da zai wanke shi daga zargi, idan ba haka ba, hukumar 'yan sanda zata yi amfani da ƙarfin doka ta kamo shi."
Tun asali matar ta fara haɗuwa da ɗan kasuwan a Facebook
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa wanda ake zargin ya fara yi wa matar barazana da Hotunan tsiraicinta da ya ɗauka.
Matar, wacce ta kasance bazawara, ta haɗu da Mista Kennedy a Facebook kuma ta ba shi kanta ya kwanta da ita a Otal lokacin da suka haɗu, ya ɗauki Hotunan ba tare da saninta ba.
Mutumin ya buƙaci N140,000 daga wurin matar a matsayin sharaɗin kar ya saki Hotuna amma bayan ta tura masa kuɗin ya gaza cika alkawarin da ya ɗauka.
Bayan Kennedy ya saki Hotuna 50, ya kara neman karin kuɗi daga wurin matar kuma ya yi barazanar sakin wasu Hotunan idan ta masa gardama.
An tattaro cewa bayan kai rahoton Kes din caji ofis ɗin Pen Cinema, wani jami'in ɗan sanda ya nemi matar ta biya N50,000 kafin ya fara mata aiki.
"Ba Zan Karɓa Ba Sai Kin Duƙa" Miji Ya Umarci Matarsa a Bidiyo, Ya Ki Karban Abinci
A wani labarin kuma Wata mata 'yar Najeriya ta sha mamaki yayin da habibinta ya umarci ta duƙa kan guiwa kafin ya karɓi abincin da ta kawo masa.
Ma'auratan sun sha dirama kan haka a wani gajeren bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta, mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu.
"Ina Kaunar Mijina Duk da Yana Bugu Na Kamar Jaka" Wata Mata Ta Nemi Saki a Kotun Musulunci, Ta Gindaya Sharaɗi 1
Asali: Legit.ng