Da Dumi-Dumi: An Halaka Wani Dan Sanda Har Lahira a Jihar Kano

Da Dumi-Dumi: An Halaka Wani Dan Sanda Har Lahira a Jihar Kano

  • Wani jami'in ɗan sanda ya rasa ransa har lahira bayan ƴan daba sun farmaki motarsu a birnin Kanon dabo
  • Ƴan daban dai sun yanka ɗan sandan ne bayan ya faɗo daga kan motar lokacin da ƴan sandan suka yi ƙoƙarin barin wajen
  • Ƴan sandan dai sun je rabon faɗa bayan rigima ta ɓarke a tsakanin wani ɗan daba da abokan hamayyarsa ƴan daba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - An halaka wani ɗan sanda wanda ba a bayyana sunansa ba har lahira a unguwar Yakasai cikin Kano Municipal a yammacin ranar Talata.

Shaidun gani da ido sun gayawa jaridar Daily Trust cewa, lamarin ya auku ne lokacin da wasu ƴan daba suka kai wa wani da ake zargin ɗan daba ne hari bayan ya sauko daga Keke Napep a wajen asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad.

Kara karanta wannan

"Ana Min Barazanar Kisa": Asari Dokubo Ya Fallasa Masu Son Ganin Bayansa a Doron Duniya

Yan daba sun halaka jami'in dan sanda a Kano
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Shaidar ganau ɗin wanda ya nemi da a sakaya sunansa ya bayyana cewa mutumin yana saukowa daga Keke Napep ɗin suka farmasa da hari.

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Lamarin ya fara ne lokacin da mutumin ya sauko daga Keke Napep, nan da nan wasu ƴan daba suka farmasa da makamai."
"An ɗauki lokaci kafin zuwan ƴan sanda waɗanda suka kasa korarsu. Ƴan daban sun koma kan ƴan sanda inda suka fara jifarsu da duwatsu."
"Lokacin da ƴan sandan suka yi ƙoƙarin kaucewa harin da gudun a yi musu ɓarna ne ɗan sandan ya faɗo nan da nan suka yi kansa inda suka yanka shi har lahira."

Ya ƙara da cewa a cikin ƴan kwanakin nan, ƴan daba masu gaba da juna sun sha ba hammata iska a unguwar, cewar rahoton Platinum Post.

Kara karanta wannan

Majiya Ta Bayyana Wanda Shugaba Tinubu Zai Iya Ba Mukamin Ministan Kudi

Ƴan sanda na gudanar da bincike kan lamarin

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna, kan lamarin ya bayyana cewa rundunar ba ta samu wani bayani ba amma ana gudanar da bincike.

"Ba mu samu wani bayani ba irin wannan amma muna bincike kan lamarin domin gano haƙiƙanin abinda ya faru." A cewarsa.

'Yan Daba Sun Halaka Wani Dan Kasuwa a Kano

A wani labarin na daban kuma, ƴan daba sun halaka wani ɗan kasuwa har lahira a jihar Kano ta hanyar caccaka masa wuƙa.

Ƴan daban dai sun halaka ɗan kasuwan ne mai suna, Alhaji Auwalu Gambo a gidansa da ke a ƙauyen Dakasoye cikin ƙaramar hukumar Garun Malam ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng