Hajjin Bana: An Fara Jigilar Alhazai Rukunin Farko Daga Saudiyya Zuwa Najeriya
- A ranar Talata ne hukumar alhazai ta sanar da fara jigilar alhazan Najeriya daga ƙasar Saudiyya zuwa Najeriya
- Mahajjata 426 waɗanda 'yan jihar Sokoto ne aka fara kwasowa daga ƙasar ta Saudiyya bayan kammala aikin hajji
- Hukumar alhazan ta ce za a samu tafiyar hawainiya wajen jigilar alhazan sakamakon cunkoson jiragen sama da ke tashi daga ƙasar ta Saudiyya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Da yammacin Talatar nan ne rukunin farko na alhazan Najeriya daga ƙasar Saudiyya suka taso daga filin jirgin sama na Jedda zuwa Najeriya a cikin jirgin Flynas Airlines mai lamba XY7402.
Mahajjatan su 426 waɗanda duk 'yan jihar Sokoto ne, sun taso ne tare da jami’in hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) guda ɗaya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ana sa ran za su iso filin tashi da saukar jiragen sama na Sultan Abubakar, da ke Sokoto da misalin karfe shida na yammacin yau a agogon Najeriya.
Hukumar alhazai ta ce za a samu tafiyar hawainiya wajen jigilar alhazan
Alhazan Najeriya 95,000 ne suka samu damar yin aikin hajjin na bana wanda aka kammala a ƙarshen makon da ya gabata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban hukumar alhazai ta ƙasa Goni Sanda, ya ce za a samu tafiyar hawainiya wajen jigilar mahajjata a makonni biyun nan na farko, saboda dokokin da Saudiyya ta sanya sakamakon cunkoson jiragen da ke tashi.
Sai dai ya ba da tabbacin cewa dukkanin jirage biyar da ke jigilar alhazan Najeriya, za su samu damar yin aiki yadda ya kamata daga baya.
Gwamnatin Abba Gida Gida ta rabawa alhazan Kano kyautar naira miliyan 65
Jaridar Leadership ta wallafa wani rahoto cewa gwamnatin Abba Gida Gida ta rabawa alhazan jihar Kano, su 6166 naira miliyan 65 kyauta.
Daraktan hukumar jin daɗin alhazai na jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu Danbappa ne ya bayyana hakan bayan wani zama da masu ruwa da tsaki a birnin Makkah.
Jarumar fim ta bayyana irin darasin da ta koya a aikin Hajji
Legit.ng a baya ta kawo muku labari kan jarumar fim ɗin kudancin Najeriya Mercy Aigbe Adeoti da ta bayyana cewa ta koyi darasi mai tarin yawa a aikin Hajjin da ta gabatar a bana.
Ta ce ta fahimci cewa a ƙasar ta Saudiyya babu nuna bambanci tsakanin talaka da mai kuɗi, ko kuma nuna wariyar launin fata.
Asali: Legit.ng