Da Dumi-Dumi: JAMB Ta Kammala Bincike Kan Mmesoma Ejikeme

Da Dumi-Dumi: JAMB Ta Kammala Bincike Kan Mmesoma Ejikeme

  • Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa an kammala bincike akan sakamakon bogi na Mmesoma Ejikeme
  • Mmesoma Ejikeme zarginta da ƙara yawan makinta na jarabawar 2023 UTME/JAMB, zargin da ta musanta duk da JAMB na ta bankaɗo hujjoji
  • Oloyede ya bayyana cewa ya sanarwa da tsohuwar ministan ilmi, Obi Ezekwesili, dangane da dambarwar damfarar da yarinyar ta samu kanta a ciki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Farfesa Ishaq Oloyede, shugaban hukumar shirya jarabawar shiga jami'a ta ƙasa (JAMB), ya bayyana cewa an kammala bincike kan Mmesoma Ejikeme, ɗalibar da ake zargi da ƙara yawan makinta a jarabawar ta 2023.

A cewar rahoto jaridar The Punch, Oloyede ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda da ya aikewa ƴan jarida daga birnin Windhoek a ƙasar Namibia.

JAMB ta kammala bincike kan Mmesoma Ejikeme
JAMB na zargin Mmesoma da yin sakamakon bogi Hoto: JAMB
Asali: Twitter

A cewar takardar, Oloyede ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Ministan Buhari a Villa, Yan Najeriya Sun Nuna Damuwa

"Maganar gaskiya ita ce JAMB ta kammala bincikenta kan batun ƙaryar makin da Nmesoma ta yi. Ba ita kaɗai ba ce aka kama cafko, sauran dai kawai sun zaɓi da kada su bayyana kansu."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

JAMB ta gano masu shirya sakamakon bogi

Oloyede ya kuma yi nuni da cewa akwai wasu ɓata-gari masu shirya sakamakon jarabawar na bogi, amma ba za su iya yin nasarar yin kutse cikin shafin na JAMB ba saboda ƙarfin tsaron da yake da shi.

Ya nuna damuwarsa kan cewa wasu ɗaliban da iyayensu ana yi musu wayau da yin sakamakon na bogi wanda a cewarsa basu san cikin cakwakiyar da ake jefasu a ciki ba.

Shugaban na JAMB ya kuma yi bayanin cewa hujjojin da suka samu daga cikin gida sun nuna cewa da haɗin bakin Mmesoma Ejikeme aka sauya mata sakamakonta.

Kara karanta wannan

Magana Ta Ƙare: Shugaba Tinubu Ya Ɗora Nauyin Dawo da Zaman Lafiya A Zamfara Kan Mutum 1

Ya ƙara da cewa akwai wasu bayanai waɗanda babu wanda ya isa ya sansu har sai idan ita ce ta bayyana musu bayanan.

Mmesoma Ejikeme Ta Yi Martani Kan JAMB

A wani labarin kuma, ɗalibar da hukumar JAMB ke zargi da ƙara yawan makinta a jarabawar share fagen shiga jami'a UTME ta 2023, ta musanta cewa ta ƙara yawan makin nata.

Mmesoma Ejikeme ta bayyana cewa a shafin hukumar JAMB ta duba sakamakon jarabawar. A cewarta ba ta san yadda ake buga sakamakon bogi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng