Garin Jan Aji: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayin Da Ya Nemi Ta So Shi Ya Koma Ga Wata

Garin Jan Aji: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayin Da Ya Nemi Ta So Shi Ya Koma Ga Wata

  • Wata budurwa yar Najeriya ta koka bayan hadadden saurayi da ya nemi soyayyarta ya koma ga wata da ta shirya amsar tayinsa
  • Matashiyar ta ce a lokacin da masoyin nata ya nemi ta zama budurwarsa, ta fada masa cewa za ta je ta yi shawara
  • Abun bakin ciki yanzu mutumin yana soyayya da wata budurwa ba tare da ya dawo ya ji shawarar da ta yanke ba, yan Najeriya sun ce ta rasa damarta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya ta garzaya soshiyal midiya domin bayyana yadda mutumin da take so ya zo ya furta mata soyayya amma ta je garin kallon ruwa kwado ya yi mata kafa.

Bayan ta gama raya ina ma ace saurayin ya tunkareta da maganar soyayya, sai ga shi sun hadu a wani biki sannan ya nuna yadda yake jin ta a ransa.

Kara karanta wannan

Fasto Ya Ki Mayar Da Kujerar Haya Bayan Ya Camfa Ta Na Tayar Da Matattu

Matashiyar budurwa
Garin Jan Aji: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayin Da Ya Nemi Ta So Shi Ya Koma Ga Wata Hoto: @Folasheycrown22
Asali: Twitter

Mutumin ya kai ga furta cewa "ina so mu fara soyayya." Matashiyar ta amsa masa sannan ta ce ya bari za ta je ta yi shawara a kai.

Ta ji takaici cewa tun daga lokacin mutumin bai dawo ba balle ya ji shawarar da ta yanke. Yan makonni bayan nan, sai ta gano ashe saurayin ya tunkari wata budurwa a makwabtansu kuma yanzu suna soyayya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli wallafarsa ta kasa:

Martanin jama'a a kan lamarin

@ScientistVivian ta ce:

"Toh da me kike tunani? Ina son koyon darasi."

@mirexmoses ta ce:

"Watakikla ya ga rubutun da kika yi a twitter inda kika yi magana kan maza."

@Ejirodkasanova ya ce:

"Kina so ki yi tunani akan me ma wai."

Matashiyar ta amsa:

"Wai na ce bari na dan ja aji kadan."

@TifeAdebayor_ ya ce:

Kara karanta wannan

Maganin yaudara: Yadda budurwa ta kassara saurayinta ta hanyar yada bayanan 'ATM' dinsa a Twitter

"Kina son wani shima yana sonki sannan ya nemi soyayyarki, idan kika amsa da eh baya nufin baki da daraja amma kawai kina son ya wahala wajen samunki, bai kamata rayuwa ya kasance da wahala haka ba."

@TifeAdebayor_ ya ce:

"Kin yi wasa da damar ki."

@sciypher:

"Mutane da dirama mara amfani. Hakan ya yi maki kyau."

Allah daya gari banban: Basarake ya auri kada a kasar Mexico

A wani labari na daban, Legit.ng ta kawo a baya cewa basaraken wani karamin kauye a kasar Mexico ya auri wata kada.

An yi wa amarya kada kwalliya da kaya irin na amare yayin da aka daure bakinta don kudin kada ta kai farmaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng