Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano Ta Kama Kwamishinan Ganduje Da Wasu Kan Badakalar Biliyan 1
- Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta damke kwamishinan ayyuka na zamanin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje
- An dai kama Injiniya Idris Wada Saleh da wasu mutane biyar kan zargin wawure kudi naira biliyan daya da sunan gyara tituna
- Bincike da hukumar yaki da rashawar ta gudanar ya nuna sam ba a yi aikin gyaran kowani titi ba sannan ba a bi ka'ida ba wajen fitar da kudin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafe ta jihar Kano ta kama tsohon kwamishinan tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan badakalar naira biliyan daya, jaridar Aminiya ta rahoto.
Shugaban hukumar yaki da rashawa na jihar da aka dawo da shi, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya yi alkawarin cewa duk wadanda ake zargi da aikata cin hanci da rashawa sai sun biya bashin abubuwan da suka aikata.
Wannan ya yi sanadiyar kamawa da tsare tsohon kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa, Injiniya Idris Wada Saleh da wasu mutane biyar kan zargin wawure naira biliyan 1.
An fitar da kudin da sunan kwangilar gyaran tituna amma ba a yi ba, bincike
An kama tsohon kwamishinan wanda ya kasance Manajan Darakta na hukumar kula da hanyoyin Kano, sakataren din-din-din, shugaban hukumar kula da harkokin gwamnati , Mustapha Madaki Huguma, daraktan kudi, daraktan bincike da tsare-tsare, da sauransu a yammacin Litinin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar yadda jaridar Daily Post ta rahoto, an kama su ne bisa zargin cire kudi sama da naira biliyan 1 domin gyara tituna 30 da magudanar ruwa a cikin birnin, ayyukan da ake zargin ba a aiwatar ba.
Wata majiya a hukumar ta bayyana cewa an biya kudaden da aka cire a rukuni uku cikin asusun kamfanoni uku a watan Afrilun 2023.
“Abin mamaki har hukumar kula da harkokin gwamnati ta bayar da takardar shaidar bayar da kwangilar bayan an biya kudin tun kwanaki goma da suka gabata wanda ya sabawa dokar sayan kayayyaki ta 2021.
"Ofishin bin tsarin ya ce sun ba da takardar shaidar amincewar ne saboda hukumar kula da hanyoyi na Kano ta ce za a gudanar da ayyukan gyara hanyoyin ne ta hanyar amfani da leburori hanyar kai tsaye amma takardun sun nuna akasin haka.
Kakakin hukumar, Abba Kabir, ya tabbatar da cewar wadanda aka kama suna amsa tambayoyi kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zaran an kammala bincike.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da daure wani dan damfara na tsawon shekaru 235
A wani labari na daban, kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin da kotun kasa ta yankewa wani matashi dan damfara.
An yankewa matashin mai suna Scales Olatunji hukuncin daurin shekaru 235 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.
Asali: Legit.ng