Ginin Bene Mai Hawa 4 Ya Rushe a Abuja, Mutane 20 Sun Makale

Ginin Bene Mai Hawa 4 Ya Rushe a Abuja, Mutane 20 Sun Makale

  • Wani gini mai hawa 4 da ake kan ginawa ya kife a birnin tarayya Abuja yau Litinin, 3 ga watan Yuli, 2023 da misalin karfe 4:00 na yamma
  • Wani ganau ya shaida cewa akalla mutane 20 sun makale a cikin ginin kuma har kawo yanzun ba'a ceto su ba
  • Jami'an hukumar kai ɗaukin gaggawa da jami'an kwana-kwana sun dira wurin domin fara aikin ceto waɗan da suka maƙale

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa ba da jimawa ba ginin wani Otal mai hawa hudu a yankin Dape, Life Camp, a birnin tarayya Abuja ya ruguje.

Wani shaida da abun ya faru a kan idonsa ya bayyana cewa ginin ya kife kan mutane sama da 20.

Bene mai hawa hudu ya ruguje.
Ginin Bene Mai Hawa 4 Ya Rushe a Abuja, Mutane 20 Sun Makale Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru da Misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2023 yayin da ma'aikata ke tsaka da aikin gina wurin.

Kara karanta wannan

Magana Ta Ƙare: Shugaba Tinubu Ya Ɗora Nauyin Dawo da Zaman Lafiya A Zamfara Kan Mutum 1

Jaridar ta tattaro cewa ginin Otal ɗin mallakin kamfanin rukunin otal otal ne wamda ake kira da sunan, Summit Villa Hotel Services.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wane hali ake ciki yanzu a wurin da lamarin ya faru?

Jaridar Punch ta tattaro cewa zuwa yanzu jami'an hukumar kai ɗaukin gaggawa (NEMA) sun dira wurin domin fara aikin ceto mutanen da suka maƙale a cikin ginin.

Haka zalika jami'an hukuma kwana-kwana ta babban birnin tarayya sun kai ɗauki wurin domin taimaka wa wajen aikin tono waɗanda suke ciki.

A halin yanzun, daraktan sashin ayyuka na hukumar kwana-kwana reshen birnin Abuja, Amiola Adebayo, ya tabbatar da rushewar ginin.

Ya ƙara da bayanin cewa har yanzun dakarun hukumar da sauran hukumomi suna kan aikin zakulo waɗanda ke ciki kuma ba zai iya cewa komai kan adadin mutanen da ibtila'in ya rutsa da su ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Ta Sha Alwashin Kakaba Wa Dalibai Harshen China A Jami'o'i, Ta Roki Alfarma

Kotu Ta Soke Korar da Jam'iyyar PDP Ta Yi Wa Tsohon Gwamna, Nnamani

A wani labarin na daban kuma Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta soke matakin da jam'iyyar PDP ta ɗauka kan tsohon gwamnan jihar Enugu.

Yayin yanke hukunci ranar Litinin, Alkalin Kotun ya ce NWC ba shi da ikon korar tsohon gwamna ko mataimaki ko kuma ɗan majalisa mai ci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel