Majiya Ta Bayyana Wanda Shugaba Tinubu Zai Iya Ba Mukamin Ministan Kudi
- Shugaba Tinubu na duba yiwuwar ba wani tsohon shugaban bankin kasuwanci daga yankin Kudu maso Yamma muƙamin ministan kuɗi
- Mutumin wanda ya fara siyasa a shekarar 2020 ana sa ran zai shiga cikin jerin ƙwararrun mutanen da shugaba Tinubu zai naɗa
- Shugaba Tinubu yana son kaucewa tsarin baya inda yake son haɗa tawaga mai kyau wacce za ta magance matsalolin da ƙasar nan ke ciki, a cewar wata majiya
Abuja - A yayin da ƴan Najeriya ke zaman dakon jiran waɗanda Shugaba Tinubu zai naɗa muƙamin minista, wani rahoto ya yi nuni da wanda za a iya naɗa wa ministan kuɗi.
A cewar Nigerian Tribune, mutumin da ake duba yiwuwar ba shi wannan muƙamin, tsohon shugaban wani bankin kasuwanci ne wanda ya fito daga yankin Kudu maso Yamma.
Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana
Jaridar tace mutumin ya kuma fara siyasa ne a shekarar 2020 sannan yana daga cikin ƙwararru waɗanda shugaba Tinubu zai naɗa muƙamin minista.
"Shugaban ƙasa yana sane da buƙatar kaucewa tsarin baya wajen naɗa ministoci. Ya nuna a jihar Legas cewa shi ya iya zaɓo ƙwararru."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ko tantama babu yana shirya tawaga mai ƙarfi wacce za ta tunkari matsalolin ƙasar nan. Nigerian Tribune ta ambato majiyar na cewa.
Jerin sunayen ministoci: Ƴan Najeriya na jiran waɗanda Tinubu zai zaɓa
Ana buƙatar Shugaba Tinubu ya zaɓi minista ɗaya daga kowacce jiha har da babban birnin tarayya Abuja, domin taimaka masa wajen tafiyar da gwamnati.
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa ministoci 44, inda wasu jihohin suka samu ministoci biyu.
Shugaban ƙasae yana da lokacin kwana 60 da zai iya kwashewa ba tare da ya kai sunayen ministoci a gaban majalisa ba, yanzu har ya ci fiye da rabin kwanakin.
Tinubu Ya Kammala Shirin Nada Ministocinsa
A wani labarin na daban kuma kun ji cewa Shugaba Tinubu ya kammala haɗa jerin sunayen ministocinsa da zai aike da su a gaban majalisa domin tantance su kama aiki.
Daga cikin ministovin da shugaban ƙasar zai naɗa ana ƙishin-ƙiahin ɗin akwai tsaffin ma'aikatan banki, Sanatoci da ƙwararun masana kan harkokin tattalin arziƙi.
Asali: Legit.ng