Gwamnan Jihar Niger Umaru Bago Ya Rushe Hukumar Zaben Jihar

Gwamnan Jihar Niger Umaru Bago Ya Rushe Hukumar Zaben Jihar

  • Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago, ya rushe hukumar shirya zaɓe mai zaman kanta ta jihar (NSIEC)
  • Gwamna Umaru Bago ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar ya fitar a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli
  • Ko a baya a shekarar 2022 majalisar dokokin jihar ta kori shugaban hukumar bisa zarginsa da aikata lafin yin ba daidai ba

Jihar Niger - Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Niger, ya rushe shugabancin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (NSIEC), rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Sanarwar rushe shugabancin hukumar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Abubakar Usman, ya fitar ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli a birnin Minna babban birnin jihar.

Gwamnan jihar Niger ya rushe hukumar zabe ta jihar
Gwamna Bago ya ce rushewar za ta fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Mayu Hoto: Abdullberqy Usman Ebbo
Asali: Twitter

A cewarsa rushe shugabancin hukumar zai fara aiki ne tun daga ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Hajji 2023: Allah Ya Yi Wa Ƙarin Alhazan Najeriya 2 Rasuwa a Makkah Ana Shirin Dawowa Gida

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Niger (NSIEC) ita ce ke da alhakin shiryawa da gudanar da zaɓen a faɗin jihar ta Niger.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin sanarwar an buƙaci mambobin hukumar da su miƙa dukkanin kayayyakin da ke hannunsu zuwa ga babban darekta ba tare da ɓata lokaci ba, cewar rahoton The Nation.

An bayyana mataki na gaba bayan korarsu

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Ana umartar mambobin hukumar zaɓen da su miƙa dukkanin kayayyakin gwamnatin jiha da ke a hannunsu zuwa ga babban darekta ba tare da yin jinkiri ba."

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rahoto cewa majalisar dokokin jihar Niger, a ranar 27 ga watan Satumban 2022, ta kori shugaban hukumar NSIEC, Alhaji Baba Aminu, bisa zargin rashin ladabi.

Gwamnan Jihar Niger Ya Gwangwaje Alhazan Jihar Da Kyautar Kudi

Kara karanta wannan

Rayuka Da Dama Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Osun

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Niger ya ba Alhazan jihar da ke gudanar da aikin Hajji a ƙasa mai tsarki kyautar makuɗan kuɗaɗe.

Gwamna Mohammed Umaru Bago ya ba Alhazan jihar kyautar Riyal 100 kowannensu domin rage ɗawainiyoyin da su ke yi a ƙasar Saudiyya wajen aikin Hajji.

Kyautar kuɗin dai ta fito ne daga asusun gwamnan ba daga lalitar gwamnatin jihar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng