Hajjin Bana: An Bayyana Ranar Da Alhazan Najeriya Za Su Fara Dawowa Gida Daga Saudiyya
- Alhazan Najeriya da suka gudanar da aikin Hajjin bana za su fara dawowa zuwa gida Najeriya bayan kammala aikin Hajjin bana
- Alhazan sama da mutum 95,000 za su fara dawowa gida Najeriya daga Saudiyya a ranar Talata, 4 ga watan Yuli
- Kowane mahajjaci an shirya zai kwashe kwanaki 40 a ƙasa mai tsarki, inda za a fara dawo da Alhazan da suka fara isa Saudiyya
Saudiyya - Alhazan Najeriya sama da mutum 95,000 da suka gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasa mai tsarki, za su fara dawowa gida daga Saudiyya a ranar Talata, 4 ga watan Yulin 2023, rahoton Leadership ya tabbatar.
Shugaban kwamitin kula da harkokin jiragen sama na hukumar jindaɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Injiniya Goni Sanda, shi ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajjin 2023 a daren ranar Lahadi a birnin Makkah.
Yadda za a yi jigilar dawo da Alhazan gida Najeriya
Ya bayyana cewa dawowar Alhazan zuwa gida za ta kasance kan tsarin farko da aka yi amfani da shi wajen zuwan Alhazan ƙasa mai tsarki, domin tabbatar da adalci.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Goni ya bayyana cewa kowane mahajjaci zai yi aƙalla kwanaki 40 a ƙasa mai tsarki kafin a dawo da su zuwa gida Najeriya.
"Za a yi amfani da al'adar wanda ya riga zuwa zai riga dawowa bisa tsari da dokokin Saudiyya na tabbatar da gaskiya da adalci." A cewarsa.
Ya roƙi Alhazan da masu jigilarsu da su gudanar da tafiyar dawowa gidan cikin tsanaki, inda ya ƙara da cewa kamfanonin jiragen sun nuna shirinsu na fara jigilar dawo da Alhazan.
A cewarsa jigilar dawo da Alhazan zuwa gida Najeriya, zai kammalu a cikin daidai lokacin da aka kwashe ana jigilar Alhazan daga Najeriya zuwa Saudiyya, face idan an samu wani abu da ka iya sanyawa a ƙara wa'adin.
Gwamnan Jihar Niger Ya Gwangwaje Alhazan Jihar Da Kyautar Makudan Kudade, Ya Daukar Musu Muhimman Alkawura 3
Gwamnan Yobe Ya Ba Alhazan Jihar Kyautar Kudi
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Yobe ga gwangwaje Alhazan jihar da ke a ƙasa mai tsarki wajen gudanar da aikin Hajji kyautar kuɗi.
Gwamna Mai Mala Buni ya ba kowannensu kyautar Riyal 300 domin su rage ɗawainiyoyin da su ke yi a Saudiyya.
Asali: Legit.ng