Sanatoci da Ma’aikatan Banki Sun Samu Shiga, An ba Buhari Kujera a Jerin Ministoci
- Jerin farko na sunayen wadanda za su zama Ministocin tarayya zai iya fitowa a farkon makon nan
- Mutanen farko da za a aikawa ‘yan majalisa sunayesu sun hada da kwararrun masana tattalin arziki
- Bayan masana tattalin arziki, Bola Ahmed Tinubu zai dauko ‘yan siyasa da Sanatocin da ke mulki
Abuja - Akwai jita-jita cewa an kusa kammala aiki kan jerin wadanda za a tantance a matsayin Ministoci, shugaban kasa ya amince da sunayen.
Nigeria Tribune ta ruwaito cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya karkare shirin gabatar da sunayen Ministocinsa zuwa ga majalisar dattawan Najeriya.
Idan labarin ya tabbata, a makon nan sunayen zababbun Ministocin zai je gaban teburan Sanatoci. Watakila daga baya a fitar da sauran Ministocin.
A jerin farko da za a fitar, za a samu kwararrun ma’aikata wadanda Bola Ahmad Tinubu yake so ya yi aiki da su domin a farfado da tattalin arziki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanatoci za su zama Minista
Tribune ta ce wadanda za su zama Ministocin sun kunshi wasu Sanatoci da ke kan mulki daga yankin Arewa da kuma kudancin kasar nan.
The Will ta ce sabon Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole zai zama Minista. Sauran wadanda ake hasashe sun hada da Rabiu Musa Kwankwaso.
Wata majiya ta ce akwai wani tsohon shugaban banki daga Kudu maso yamma wanda ya shiga siyasa a ‘yan shekarun bayan nan da za a ba Minista.
Bola Tinubu ya na so masana su cikin majalisar FEC, a maimakon ya tara ‘yan siyasa a gwamnati.
Sabon shugaban kasar zai yi kokarin shawo kan sabanin tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje wajen rabon mukamai.
Wani fitaccen ‘dan adawa da zai iya shiga gwamnatin Bola Tinubu ne shi ne tsohon Gwamna Nyesom Wike da wasu daga cikin ‘yan kungiyar G5.
Akwai yiwuwar Tinubu ya tausayawa tsofaffin Gwamnoni da su ka kunyata a zaben 2023, su ka gagara tsaida magada kuma su ka fadi takarar Sanata.
An ba Buhari kujera daya?
An samu rahoto cewa Bola Tinubu ya yi wa Muhammadu Buhari alfarma, ya ce ya tura sunan wanda yake a ba kujerar Minista daga jihar Katsina.
Ana jita-jita cewa Buhari ya aika sunan wani, sai dai tsohon shugaban kasar ya nanata cewa bai da niyyar tsoma bakinsa cikin mulkin Tinubu.
Asali: Legit.ng