Tsohon Shugaba Buhari Ya Tura Sunan Wanda Yake So a Ba Minista a Mulkin Tinubu Daga Jihar Katsina
- Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da shawarar wanda ya dace Tinubu ya ba mukamin minista daga jihar Katsina
- Ana bukatar Tinubu ya zabo minista daga kowace jiha a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya da za su taimaka masa wajen tafiyar da mulkin kasar
- A lokacin Buhari ya nada ministoci 44, inda wasu jihohin suka samu mukaman ministoci biyu
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya tura sunan wanda ya kamata shugaba Bola Tinubu ya nada a matsayin minista daga jihar Katsina.
Ana bukatar Tinubu ya nada minista daga kowace jiha a jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja domin taimaka masa wajen tafiyar da gwamnatin kasar nan.
Buhari ya nada ministoci 44 a zamaninsa, yayin da wasu jihohi suka samu ministoci biyu.
A cewar jaridar Nigerian Tribune, Tinubu ya karramawa Buhari ta hanyar ba shi damar gabatar da wanda yake so a ba kujerar minista daga jihar Katsina.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar majiyar, tuni tsohon shugaba Buhari ya girmama karramawar, kuma an ce ya aike da sunan wani ga magajinsa.
Sai dai, ya zuwa yanzu, bamu samu labarin wanda aka ce shine Buhari ya mika sunansa ba, haka nan, ba a ji daga bakin masu sharhi kan shiyasar Najeriya ba ko akwai wanda suke tunanin shi za a ba.
Majiya ta bayyana wanda Tinubu zai iya nadawa a matsayin ministan kudi
A bangare guda, akwai yiwuwar Tinubu ya nada wani tsohon babban jami’in bankin kasuwanci daga yankin Kudu maso Yamma ya zama ministan kudi.
Mutumin, wanda ya shiga siyasa gadan-gadan a shekarar 2020 kuma kwararren akanta, ana sa ran zai kasance cikin wadanda shugaban zai nada.
Tinubu, a cewar wata majiya, yana da burin yin watsi da tsohon tsarin daukar ministoci tare da nada wadanda suka kware a fannin da ya dace.
Tinubu ne zai yi nasara a kotun kararrakin zabe
A wani labarin, kunji yadda aka bayyana yiwuwar Tinubu ya yi nasara a kotun zabe, kamar yadda jigon APC ya bayyana.
A cewarsa, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na APC suna bata lokaci ne kawai a kotun, saboda basu da hujjoji.
An maka Tinubu, INEC da APC a kotu tun bayan kammala zaben shugaban kasa na 2023 saboda zargin dulmuyel a zaben.
Asali: Legit.ng