Daliba Ta Yi Karyar Cin Maki 362 a Harrabawar JAMB, Ta Samu Kyautar Naira Miliyan 3 Daga Kamfanin Innoson

Daliba Ta Yi Karyar Cin Maki 362 a Harrabawar JAMB, Ta Samu Kyautar Naira Miliyan 3 Daga Kamfanin Innoson

  • Hukumar shirya jarrabawa ta JAMB ta bayyana cewa, za ta dauki mataki kan wata dalibar da ta ce ta ci maki mai yawa
  • Hukumar ta gano cewa, matashiyar ta samu maki 249 ne ba 362 da take yada ta samu ba, kamar yadda rahoto ya bayyana
  • A baya, dalibar ta samu kyautar kudade daga wani kamfanin mota a Najeriya, lamarin da ya dauki hankali matuka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta ce za ta janye sakamakon jarrabawar da Ejikeme Joy Mmesoma ta yi na UTME.

Hukumar ta ce matashiyar ta samu maki 249 ne a jarabawar sabanin 362 da ta ke ta yadawa ta samu a baya, The Nation ta ruwaito.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugabanta na fannin hulda da jama’a Fabian Benjamin ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Kara karanta wannan

Binciko gaskiya: Shin da gaske ne za a kara wa Tinubu, Shettima da 'yan siyasa albashi?

Daliba ta yi karyar cin maki 362 a JAMB, za a dauki mataki
Dalibar da ta yi karyar cin makin JAMB | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Za mu dauki mataki, inji hukumar JAMB

Hukumar ta ce za ta titsiye Ejikeme bisa laifin jirkita sakamakon da ta samu a jarrabawar da JAMB din ta shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, Ejikeme ta samu tallafin Naira miliyan 3 daga wanda ya kafa kamfanin Innoson Motors, Innocent Chukwuma saboda ta samu maki 362 a UTME na 2023, rahoton Leadership.

Hukumar ta gargadi ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan da wadanda suka rubuta jarabawar UTME kuma suke karyar sun samu maki mai yawa.

Yadda jarrabawar UTME take a Najeriya

A Najeriya, jarrabawar UTME da JAMB ke shirya na daya daga matakan da dalibai ke wucewa kafin shiga makarantun gaba da sakandare.

Akan nuna damuwa wajen rasa maki mai yawa a jarrabawar, wacce dole dalibi ya sake maimatawa bayan shekara guda, kamar yadda hukumar JAMB ta tanada.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Daba Suka Caccaki Wani Dan Kasuwa Har Lahra a Jihar Kano

Haka nan, wasu kan yi karyar samun maki mai yawan da ya wuce misali don burgewa jama’ar da suke son burgewa.

Yarinya 'yar shekara 16 ce ta fi kowa cin JAMB a 2023 da maki 362

A wani labarin, wata daliba a makarantar sakandaren mata ta Anglican da ke Nnewi a jihar Anambra, Ejimeke Joy ya dauki hankalin jama’a bayan lashe maki mai tsoka jarrabawar UTME.

Rahoton da Legit.ng Hausa ke samu ya bayyana cewa, dalibar ta samu maki 362 a jarrabawar da hukumar JAMB ke shirya a duk shekara.

Wakilinmu a jihar Anambra, Mokwugwo Solomon ya gano adadin makin da dalibai ta samu kan kowane darasi da ta rubuta a jarrabawar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.