“Ya Ci Amana Ta”: Mata Sakin Bayanan Katin Ciran Kudin Saurayinta a Twitter Don Ta Yi Maganinsa

“Ya Ci Amana Ta”: Mata Sakin Bayanan Katin Ciran Kudin Saurayinta a Twitter Don Ta Yi Maganinsa

  • Wata budurwa ta jawo cece-kuce a shafin sada zumunta yayin da take koyawa saurayinta darasi kan cin amanarta da ya yi
  • Ta saki hoto da bayanan katin cire kudinsa a shafin Twitter kuma ta karfafawa madatsa gwiwar su sayi abin da suke so da katin
  • Lamarin dai ya jawo cece-kuce, inda wasu suka yi kokarin sayen abubuwa da katin, wasu kuwa suka yi ta sukar matakin da ta dauka

Wata budurwa mai suna Chloe a shafin Twitter ta saki bayanan katin cire kudi na saurayinta a dandalin sada zumunta da muhawara a yunkurinta na yin maganinsa.

A cewar Chloe, saurayin nata ya ci amanarta kuma hakan ne ma ya kai ga ta aikata yada bayanan katin. Ta bukaci kowa da ya ga katin ya yi siyayya da shi a kantunan yanar gizo.

Kara karanta wannan

“Kamar a Fim”: Matashiya Ta Auri Hadadden Dan Koriya a Asiya, Hadadden Bidiyon Bikin Ya Zautar Da Yan Mata

Mutane da yawa sun bi abin da ta fada, inda suka yi siyayya tare da bayyana abin da suka siya da kuma yabawa saurayin. Ta ce duk ranar Lahadi ake biyansa a wurin aiki.

Yadda budurwa ta kassara saurayinta bayan ya samu matsala da ita
Budurwa ta kassara saurayinta da ya ci amanarta | Hoto: Tom Grill, Twitter/@selfishfooIs
Asali: Getty Images

Akwai duk da haka, wadanda suka ji tausayin saurayin kuma suka soki budurwar saboda abin da ta aikata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rubutun da ta yada ya yi matukar yaduwa, amma daga baya aka ga an goge shi saboda wasu dalilai.

Martanin jama’a a kafar Twitter

Epische Kerl:

“Dan uwa ya yi sanya a yawa, wannan katin cire kudi ne na CashApp, tabbas yana karbar sakon cire kudi.
“Kamata ya yi ya gaggauta toshe katin kana ya datse duk wani ciniki, ya kamata ya yi hakan cikin gaggawa da ganin cire kudi na farko. Abin takaici.

Banjo Tee:

Kara karanta wannan

Allah Daya Gari Banban: Yadda Aka Sha Shagalin Bikin Wani Basarake Da Amaryarsa Kada

“Wannan kariyar ta kashe wannan mutumin, kowane namiji na cin amana a yanzu kuma haka wasu matan zamani. Don haka, kamata ya yi ta kwantar da hankali ta yi rayuwarta, watakila ma budurwarsa ce kawai ba ma mata ba.”

Opeyemi Michael Mahwii:

“Duk wadannan martanin wasa ne kawai. Babu wanda zai iya sayen komai.
“Sun yi nasarar yin oda ne, amma an datse saboda ba a saka adireshin biya ba don haka bai zama sahihi ba."

Saalim Aremoh:

“Wannan rashin hankali ne na karshe don miji ko saurayi ya ci amanarki shikenan abu na gaba kawai ki yada bayanan katinsa a yanar gizo a lokacin da zai fita fa ya ba ki umarnin cefane da katin, bai kamata mutum ya kasance da butulun mace irin wannan ba.”

Felix C. Okorie:

“Ya danganta da wa take rayuwa duk da haka...
“Watakila lusari ne ko kuma wanda bai san me yake ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Fitaccen malamin addini a Najeriya ya fadi a filin jirgin sama saboda tsananin rashin lafiya

“Saboda dole za ta girbi abin da ta shuka.”

An dai kusa samun raguwar yada bayanai a Twitter, domin mai kamfanin ya ce zai sanya takunkumi ga adadin rubutun da ake karanta nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.