Rayukan Bayin Allah Da Dama Sun Salwanta a Wani Sabon Rikicin Kabilanci a Jihar Taraba

Rayukan Bayin Allah Da Dama Sun Salwanta a Wani Sabon Rikicin Kabilanci a Jihar Taraba

  • Sabon rikicin ƙabilanci ya sake ɓarkewa a jihar Taraba a tsakanin ƙabilun Karimjos da Wurkuns a ƙaramar hukumar Karim Lamido
  • Aƙalla rayukan mutum 50 ne suka riga mu zuwa gidan gaskiya a sabon rikicin wanda ya ɓarke a daren ranar Asabar
  • Hukumomi sun tabbatar da aikewa da jami'an tsaro zuwa yankin da ake rikicin domin dawo da doka da oda

Jihar Taraba - Aƙalla mutum 50 suka rasa rayukansu sannan aka ƙona gidaje da dama a wani sabon rikicin ƙabilanci a jihar Taraba.

Jaridar Premium Times tace shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa rikicin ya ɓarke ne a ranar Asabar, 1 ga watan Yuli, a ƙaramar hukumar Karim Lamido ta jihar.

Sabon rikicin kabilanci ya barke a jihar Taraba
Akalla mutum 50 aka halaka a rikicin Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Amma ƴan sandan sun bayyana cewa ba za a iya tantance yawan rayukan da suka salwanta ba ya zuwa yanzu har sai an kammala bincike.

Kara karanta wannan

Rayuka Da Dama Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Osun

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Usman Abdullahi, ya bayyana cewa sabon rikicin ya ɓarke a tsaknin ƙabilun Karimjos da Wurkuns da misalin ƙarfe 3:00 na dare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A cikin ƴan kwanakin nan da suka wuce an yi ta kai hare-haren ramuwar gayya a wasu ƙauyakun yankin, inda Karimjos kd farmakar Wurkun, sannan Wurkuns su farmaki Karimjos, ko Wurkuns su farmaki Karimjos, su ma sai mi rama farmakin da aka kai musu." A cewarsa.

An aike da tawagar jami'an tsaro zuwa yankin

Abdullahi ya yi nuni da cewa na tura tawagar jami'an tsaro ta ƴan sanda da sojoji domin dawo da doƙa da oda a yankin, cewar rahoton The Independent.

Waɗannan kashe-kashen da asarar dukiyoyin da suka haɗa da gidaje, gonaki da dabbobi na zuwa ne sato ɗaya bagan gwamnan jihar, Kefas Agbu ya gana da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro kan buƙatar samar da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: "Ku Ji Tsoron Allah" Manyan Malamai Sun Aike da Muhimmin Saƙo Ga Sabbin Shugabanni

Hausawa Sun Koka Kan Kisan Mutanensu a Taraba

A wani labarin kuma, al'ummar Hausawa a ƙaramar hukumar Takum ta jihar Taraba sun nemi hukumomi da su bi musu kadin mutanen da aka halaka musu.

Hausawan dai sun yi zargi ƴan ƙabilar Kuteb da halaka mutum 32 waɗanda basu ji ba basu gani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng