Dan Najeriya Da Bashi Ya Yi Wa Katutu Ya Koka Bayan Matarsa Ta Shekaru 12 Ta Yi Watsi Da Shi Kan Ragon Sallah
- Wani magodanci dan Najeriya ya koka kan abubuwan da matarsa ta shekaru 12 ta ke yi masa
- Mutumin ya bayyana cewa matarsa ta daina yi masa magana sannan ta ki girkawa yaran abinci saboda ya gaza siya mata ragon Sallah
- Ya ba da labarin yadda bata nuna masa kauna da tallafa masa idan yana cikin mawuyacin hali sannan ya yi magana kan rabuwa da ita
Wani magidanci dan Najeriya ya koka cewa matarsa ta ki girkawa yaransa abinci ko yi masa magana saboda ya gaza siya mata ragon Sallah.
Abdullahi Misilli, ma'aikacin gwamnati wanda ya ba da labarin daga dan jarida Lawan Bukar Maigana a Twitter, ya ce mutumin bai raba fashin siyan rago ba duk lokacin bikin babban Sallah tsawon shekaru 12.
Sai dai kuma, tarin bashin da ke kansa da kudin makarantar yara ya hana shi siyan rago a 2023 amma matar ta ki fahimtarsa.
Tsadar Mai: Magidanci Ya Saki Daya Daga Cikin Matansa, Ya Mayar Da Dayar Gida Saboda Matsin Tattalin Arziki
Mutumin ya bayyana cewa zai siya mata dan karamin rago amma ya ce bata sonsa domin bata taba tallafa masa ba idan ya shiga matsin rayuwa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ina da 100k a aljihuna. Zan je na siya mata dan karamin rago amma Allah ya sani cewa matata bata sona saboda bata taba tallafa mani ba idan na shiga matsin rayuwa," inji mutumin.
A cewar mutumin, bai saki matarsa ba tukuna saboda yaran.
Kalli wallafar a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Erbdoul ya ve:
"Allah ya taimake mu, amma magana ta gaskiya yara ne dalilin da yasa wasu maza (idan ba duka ba) sauya tunani idan maganar saki ya shigo. Kuma abun takaici, abun takaici zai zamana akwai matsala. Don haka hakuri ne kawai abun yi amma yana da wahala."
@imran_MUFC ya ce:
"Bayan kowace Salla ina yawan yi wa matata addu'a idan ba haka ba da na shiga bashin da ya fi karfina. Ina tara kudi a hannunta don siyan ragon Sallah amma yan kwanaki kafin Sallah, matar nan ta ce lallai kada mu siya cewa muna da wasu bukataun yi."
@sadiqsolar ya ce:
"Kada ya siyan mata amma ya kalle shi a matsayin Ibadar da yake sannan idan bai da hali a wannan lokacin, ba wajibi bane a kansa."
Legit.ng ta zanta da wasu magidanta don jin yadda abun ya kaya tsakaninsu da iyalinsu a lokacin layya.
Mallam Ahmadu ya ce:
"Alhamdulillah mungode Allah kan yadda abubuwa suka kasance, tabbass samun mace mai fahimta yana da matukar amfani a gidan aure. Ban samu yi wa iyalina layya ba amma akwai fahimta sosai a tsakaninmu. Makwabta sun taimaka sosai domin sun kawo mana sadaka kuma ko a fuska maidakina bata nuna rashin jin dadi ko damuwa ba.
"Hasalima ita ta karfafa mun gwiwa cewa mu godewa Allah tunda mun yi sallar cikin koshin lafiya."
A bangarensa mallam Abubakar kuwa cewa ya yi:
"Bana sai godiya kawai, na samu yi wa iyalina layya koda dai ragon ba wani mai girma bane, amma ta nuna jin dadi da godiyarta a kan abun Allah ya sawwake mana."
Daga neman a kawo mata yar aiki, uwar miji ta kaiwa matar danta karamar yarinya
A wani labari na daban, wata matar aure yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya kan yarinyar da uwar mijinta ta kawo mata.
Ta wallafa wasu jerin bidiyoyi na karamar yarinyar tana bacci tare da jinjirinta a kan gado.
Asali: Legit.ng