Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Kange Matarsa Na Tsawon Shekaru Biyu, Baya Bata Abinci

Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Kange Matarsa Na Tsawon Shekaru Biyu, Baya Bata Abinci

  • Yan sanda sun kama Abdullahi Isa a garin Maiduguri da ke jihar Borno kan zarginsa da cin zarafin matarsa
  • Ana zargin Isa da kange matarsa har tsawon shekaru biyu sannan baya bata abinci yayin da take tsare a gidansa
  • Makwabta ne ke satar hanya suna taimaka mata da abun da za ta ci har zuwa lokacin da asirinsa ya tonu

Borno - Rundunar yan sanda ta kama wani mutum mai suna Abdullahi Isa kan cin zarafi, kullewa da kuma horar da matarsa da yunwa na tsawon shekaru biyu a garin Maiduguri, jihar Borno a ranar Juma'a.

Jaridar Daily Trust ta tuntubi mai rajin kare hakkin mata da yara, Kwamrad Lucy D. Yunana wacce aka gani a wani bidiyo da aka kwashi matar zuwa asibiti inda ta ce abun ya faru ne a yankin Gwange 3na Maiduguri.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Daba Suka Caccaki Wani Dan Kasuwa Har Lahra a Jihar Kano

Magidanci da ya kange matarsa
Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Kange Matarsa Na Tsawon Shekaru Biyu, Baya Bata Abinci Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yadda magidanci ya kange matarsa ta sunna har tsawon shekaru biyu

Ta yi bayanin cewa Bulama na Gwange (3) ya dauki ma'aikatanta zuwa gidan wanda ake zargin, inda a nan ne aka rufe matar na tsawon kimanin shekaru biyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wanda ake zargin mai suna Isa Abdullahi na Gwange (3) a garin Maiduguri ya kasance mijin matar wacce aka boye sunanta.
"An sanar da mu cewa makwabta ne ke ciyar da ita, ba a bata abinci amma yawancin lokuta makwabta kan saci hanya su bata abinci.
"Abun godiya, ma'aikatanmu suna gudanar da aikin wayar da kan jama'a kanSGBV a Gwange lokacin da Bulaman yankin ya kai ma'aikatanmu gidanda aka rufe ta kuma abun da suka gani ya yi muni sosai kuma hakan ya sa muka gaggauta sanar da hukumar da ta dace don ceto rayuwar matar.

Kara karanta wannan

Mutane 6 Sun Rasu a Borno Yayin Da Wani Bam Da 'Yan Boko Haram Suka Binne a Kan Hanya Ya Tashi

"Mun je chan tare da shugabar hukumar kare hakkin dan adam, Barista Jumai Mshelia sannan suka gan ta a dakin, abun da muka gani a dakin ya yi muni da yanayi kamar ba mutum. Jami'an yan sandan Gwage sun kama mutumin kuma yanzu haka yana ofishin yan sanda."

Matar da asibiti tana samun kulawar likitoci

Kwamrad Lucy ta kara da cewar ta tuntubi mutanen da ya kamata kuma an dauki matar zuwa asibiti don bata kulawa kuma yanzu likitoci na aiki a kanta.

Sai dai wanda ake zargin, Isa Abdullahi ya yi ikirarin cewa yaranzu bakwai tare amma duk sun mutu kuma matar tasa na fama da aljanu wanda shine dalilin da yasa ya rufe ta.

Yan daba sun halaka wani dan kasuwa a Kano

A wani labari na daban, mun ji cewa tsagerun yan daba sun farmaki wani dan kasuwa a gidansa da ke kauyen Dakasoye na jihar Kano.

Maharan da suka kai wa mamacin hari cikin dare, sun ta sukar mutumin da wuka har sai da ya rasa ransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng