Gwamnan Jihar Niger Ya Gwangwaje Alhazan Jihar Da Kyautar Makudan Kudade, Ya Daukar Musu Alkawura 3

Gwamnan Jihar Niger Ya Gwangwaje Alhazan Jihar Da Kyautar Makudan Kudade, Ya Daukar Musu Alkawura 3

  • Gwamnan jihar Niger Mohammed Umaru Bago ya ba Alhazan jihar kyauta mai tsoka a ƙasa mai tsarki wajen aikin Hajji
  • Gwamna Bago ya ba kowannensu kyautar Riyal 100 yayin da ya ba ma'aikata kyautar Riyal 200 kowannensu
  • Gwamman ya kuma sha alwashin ƙara inganta walwala da jindaɗin Alhazan jihar nan gaba inda zai yi wasu muhimman ayyuka uku

Saudiyya - Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago, ya gwagwanje Alhazan jihar da kyauta mai tsoka a ƙasa mai tsarki lokacin aikin Hajjin bana.

Gwamnan ya ba Alhazan jihar ta Niger waɗanda yawansu ya kai 3710 kyautar Riyal 100 kowannen su.

Gwamnan jihar ya ba Alhazan jihar kyautar Riyal 100 kowannensu
Gwamnan ya bayar da kyautar kuɗin ne daga aljihunsa Hoto: Abdullberqy Usman Ebbo
Asali: Twitter

Riyal 100 a kuɗin Najeriya sun kai N25,000.

Gwamnan ya kuma ba ma'aikata mutum tara, ma'aikatan wucin gadi mutum 25 da masu sanya ido 25 da shugabannin ƙananan hukumomin suka zaɓo, Riyal 200 kowane daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Bayan An yi Rashin Wani Babban Likita a Arewacin Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan kan ɓangaren sadarwa, Abdulberqy U Ebbo, ya fitar a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 1 ga watan Julin 2023.

Gwamnan ga bayar da kyautar ga Alhazan ne lokacin da ya ziyarcesu a Mina, inda ya tabbatar da cewa kyauyar ta fito ne daga aljihunsa ba daga aljihun jihar Niger ba.

Gwamna Bago ya ce ya yi musu kyautar ne bisa yabawa da ya yi da halin dattako da wakilai nagari da suka zama na jihar a ƙasa mai tsarki.

Gwamna Bago ya ɗaukar musu alƙawura uku

Gwamna Bago ya kuma tabbatarwa da Alhazan cewa gwamnatin jihar na bakin ƙoƙarinta wajen inganta aikin Hajji daga shekara mai zuwa, inda za ta fara da gyara sansanin Alhazai da gyara filin tashi da saukar jiragen sama na jihar da ke a birnin Minna, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Ziyarci Sarkin Musulmi, Ya Nemi Alfarma 1 Tak

Gwamnan ya kuma ƙara da cewa za a tabbatar Alhazan suna samun ababen hawa masu kyau a ƙasa mai tsarki.

Daga ƙarshe ya yi addu'ar Allah ya amsa ibadar da suka gabatar ya kuma ba jihar Niger dauwamammen zaman lafiya da ci gaba shekaru masu zuwa.

Gwamnan Bauchi Ya Ba Alhazan Jihar Kyauta a Saudiyya

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Bauchi ya gwangwaje Alhazan jihar da kyautar maƙudan kuɗade a ƙasa mai tsarki.

Gwamna Bala Mohammed ya ba kowannensu kyautar Riyal 300 domin rage raɗaɗin kuɗaɗen da su ke kashewa a Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel