Hawaye Sun Kwaranya Bayan An yi Rashin Babban Likita a Jihar Bauchi
- An shiga jimami a jihar Bauchi biyo bayan rasuwar babban likita kuma likitin jijiya na farko a jihar da ke Arewacin Najeriya
- Farfesa Abdu Ibrahim ya koma ga mahaliccinsa ne bayan ya yi doguwar jinya a asibitin koyarwa na ABUTH da ke a Bauchi
- Gwamnan jihar Bala Mohammed ya aike da saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar likitan inda ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga jihar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Bauchi - Likitin jijiya na farko daga jihar Bauchi, Farfesa Abdu Ibrahim, ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa, Farfesa Abdu Ibrahim ya koma ga mahalaiccinsa ne ranar Alhamis a asibitin koyarwa na jami'ar Sir Abubakar Tafawa (ABUTH) da ke a Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, wanda yake ƙasar Saudiyya wajen aikin Hajji, ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalai, ƴan'uwa da abokai na marigayin, cewar rahoton PUNCH.
Kano: Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Ce Bai Kori Ma'aikata 10,800 Ba, Ta Bayyana Dalilan Dakatar Da Albashinsu
Rasuwarsa babbar asara ce ga al'ummar jihar Bauchi, Gwamna Bala
Ya kuma bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ba kawai ga iyalansa ba, har da al'ummar jihar Bauchi da ƙasa baki ɗaya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnan a cikin wani saƙo da hadiminsa na musamman kan watsa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Juma'a, ya bayyana cewa marigayin ya taimaka sosai wajen bunƙasa ɓangaren kiwon lafiya a jihar Bauchi.
Ya bayyana cewa za a riƙa tunawa da Farfesa Abdu Ibrahim a jihar bisa jajircewarsa da tsayawa kai da fata wajen kawo ci gaba a fannin kiwon lafiya tun bayan da aka kafa jihar.
Wani ɓangare na saƙon na cewa:
"Gwamna Bala Mohammed, a madadinsa da na iyalansa da gwamnstinsa da al'ummar jihar Bauchi, yana miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalai, ƴan'uwa da abokan aiki da gaba ɗaya al'ummar jihar Bauchi."
"Ya yi addu'ar Allah ya sanya ya yi masa rahama da Aljanna firdaus sannan yaba iyalansa da al'ummar jihar Bauchi, haƙurin jure wannan rashin da aka yi."
Babban Sanatan Najeriya Ya Kwanta Dama
A wani labarin kuma, an yi rashin wani babban Sanatan Najeriya mai ƙarfin faɗa a ji wanda ya wakilci Anambra ta tsakiya a majalisar dattawa daga shekarar 2007 zuwa 2011.
Sanata Annie Okonkwo ya yi bankwana da duniya yana da shekara 67 a wani asibiti a ƙasar Amurka.
Asali: Legit.ng