“Ya Tafi Landan Ne Don Jinya Kamar Yadda Ya Saba”, Rafsanjani Ya Caccaki Buhari
- An caccaki tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan barin Najeriya da ya yi zuwa birnin Landan
- Tsohon hadiminsa ya bayyana cewa Buhari ya bar mahaifarsa ta Daura zuwa Landan don kauracewa hayaniya
- A halin da ake ciki, dan fafutuka Auwal Musa Rafsanjani ya yi zargin cewa tsohon shugaban kasar na Landan don yin jinya kamar yadda ya saba
FCT, Abuja - Ana tsaka da cece-kuce kan barin mahaifarsa ta Daura da ke jihar Katsina da ya yi, inda ya koma Landan, wani sabon bayani ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana kasar Turai inda yake ganin likita kamar kullun.
Ku tuna cewa a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni, Garba Shehu, tsohon hadimin Buhari, ya ce tsohon shugaban kasar ya tafi Landan saboda ya kaucewa hayaniya saboda baya jin dadin yadda mutane ke yi masa zarya.
Shehu ya bayyana a cikin wata sanarwa:
"Ya zabi komawa gida a Daura, yana mai fatan samun irin yanayin da yake sowa kansa na rashin hayaniya amma sai ya gane cewa wannan ba shine abun da ya faru ba, baki na ta zarya safe, rana da dare, ya tafi wani wuri mai nisa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Wannan shine fatansa cewa a barsa ya samu isasshen hutun da yake bukata da kuma ba gwmanatin Tinubu yanayin da ya dace domin aiki kan cimma alkawaran da suka dauka."
Buhari na Landan don jinya - Rafsanjani
Da yake martani ga jawabin Shehu, mai rajin kare yancin dan adam kuma dan fafutukar yaki da rashawa, Auwal Musa Rafsanjani ya fada ma Legit.ng cewa da yiwuwar tsohon shugaban kasar ya tafi Landan ne don jinya yadda ya saba.
Ya bayyana cewa bai yi mamaki ba da ya ji cewa tsohon shugaban kasar na Landan domin halinsa ne koda yake matsayin shugaban kasa.
Rafsanjani ya ce:
"Ban yi mamaki ba cewa tsohon shugaban kasar ya sake tafiya Landan saboda ya kasance abun da ya dunga aikatawa koda yake matsayin shugaban kasar.
"Na yarda cewa ya tafi Landan jinya kamar yadda ya saba. Ina ganin cewa wannan shine abun da ya faru a zahirin gaskiya. Banbancinsa da yanzu kawai shine ba lallai da kudaden kasar za a yi amfani wajen kula da shi ba."
Rafsanjani ya daura laifin halin da Najeriya ke ciki a kan tsohon shugaban kasar, yana mai cewa satar da yan majalisarsa suka tafka ne ya lalata kasar zuwa yadda take a yanzu.
Ya ce:
"A bayyane yake karara cewa Buhari ya gaza a wurare da dama kuma kuna iya ganin cewa ministocinsa da dama na guduwa kuma wasun su na karkashin bincike...karara ya nuna yan Najeriya basu gamsu da kokarinsa ba."
Buhari ya koma waje mai niya don kauracewa hayaniya, Garba Shehu
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Garba Shehu ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar mahaifarsa da ke Daura, jihar Katsina.
Shehu ya yi bayanin cewa Buhari ya bar Daura zuwa wata uwa duniya saboda ya gaza samun shirun da yake son samu bayan barin mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng