Hargitsi Ya Tashi Kan Aikin Kula da Kare Da Aka Sanya Wa Miliyan N104m Duk Shekara

Hargitsi Ya Tashi Kan Aikin Kula da Kare Da Aka Sanya Wa Miliyan N104m Duk Shekara

  • Abun mamaki baya karewa a duniya, ana neman wanda zai riƙa kula da karnuka kan kuɗi kusan miliyan N100m a shekara
  • Kamfanin da ya buga sanarwan neman aiki a ƙasar Ingila ya bayyana irin aikace-aikacen da mai kula da karen zai yi
  • Sai dai mutane sun yi tururuwar neman aikin wanda sai da ta kai ga goge sanarwan saboda yawan masu turo takardar nuna sha'awa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani kamfanin ɗaukar ma'aikata a ƙasar Burtaniya, Fairfax and Kessington, ya ga babban abin mamaki jim kaɗan bayan sanar da neman mai kula da karnuka a shafinsa.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa a shelar neman aiki da kamfanin ya fitar, ya ce ana neman wanda zai iya kula da wasu karnuka kan albashin dala dubu 127,000 a kowace shekara.

Neman aikin kula da kare.
Hargitsi Ya Tashi Kan Aikin Kula da Kare Da Aka Sanya Wa Miliyan N104m Duk Wata Hoto: aminiya
Asali: UGC

Waɗannan makudan kuɗi idan aka musanya su zuwa kuɗin naira ta Najeriya sun kai kimanin miliyan N97m da wasu 'yan dubbanni a sama.

Kara karanta wannan

Ana Shagalin Babbar Sallah, Gwamna Ya Dakatar da Wasu Ma'aikata da Babban Shugaba Nan Take

Bayanai sun nuna cewa wannan aiki kan zunzurutun kuɗi masu yawa haka a ƙasar Ingila ya kusa haddasa hargitsi a tsakanin masu kula da dabbobi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Aikace-aikacen da ake bukatar mai kula da karnukan ya riƙa yi

Haka zalika sanarwa ɗaukar aiki ta jero ayyukan da ake tsammanin duk wanda aka ɗauka zai riƙa yi wa karnukan wanda ya haɗa da zama tare da masu karnukan.

Bayan haka mai kula da karen shi ke da alhakin kula da lafiyarsu, ba su kariya da kula da abinda zasu ci da kuma abinda zasu sha.

Bayan haka, duk wanda aka ɗauka aiki zai riƙa tabbatar da suna motsa jiki domin inganta lafiya, ya kai su wurin likata a duk lokacin da aka gindaya da kuma sanya su nishaɗi da walwala.

Bugu da ƙari, mai kula da karen shi zai riƙa raka su zuwa duk wata tafiya da zasu yi a ciki da wajen ƙasar Ingila.

Kara karanta wannan

Miliyan 1 Na Ke Ware Wa Jami'an Kan Hanya Yayin Jigilar Shanu Daga Arewa Zuwa Kudu, In Ji Isiaka

Mutane sun yi tururuwar neman aikin

Jim kaɗan bayan wallafa shelar neman wanda zai yi wannan aiki, kamfanin ya ce ya samu akalla mutane 3,000 da suka tura takardar suna sha'awar wannan aiki ta Intanet.

Da yake zantawa da jaridar New York times, wacce ta fara wallafa labarin, George Dunn ya ce:

"Karo na farko kenan da muka taba samun irin wannan domin idan ka yi la'akari da yawan kudin, ko kwararren likitan dabbobi ba zai iya haɗa su a shekara ba."

Sai dai bai fayyace ko sun ɗauki ma'aikacin ko a'a ba, ya ce bisa tilas suka goge sanarwan a shafinsu saboda tururuwar neman aiki har ta kai mutane dubanni.

Matashi Mai Samun N100k Ya Bukaci Budurwa Mai Samun N34m Ta Aje Aikinta Ta Aure Shi

A wani labarin kuma Wata matashiya ƴar Najeriya ta bayyana yadda ta kaya tsakaninta da wani matashi wanda ya ke son ya aure ta.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Waliyyin Amarya Ya Sace Sadakin Amarya Ana Shirin Daura Aure a Masallaci

Budurwar ta bayyana cewa matashin yana samun N100k zuwa N200k a shekara yayin da ita kuma ta ke samun N34m amma duk da haka ya ce ta aje aiki su yi aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262