Falana Ya Bukaci DSS Ta Hanzarta Bincike, Ta Gurfanar da Bawa da Emefiele a Kotu

Falana Ya Bukaci DSS Ta Hanzarta Bincike, Ta Gurfanar da Bawa da Emefiele a Kotu

  • Femi Falana, babban lauya mai fafutukar kare hakkin ɗan adam ya buƙaci DSS ta gaggauta kammala bincike kan Bawa da Emefiele
  • Ya ce ci gaba da tsare su ba tare da gurfanar da su a gaban shari'a ba ya saɓa kundin dokokin aikata manyan laifuka
  • Falana ya roƙi gwamnatin tarayya ta tafiyar da lamarin kan doka domin guje wa faɗawa wata matsalar

FCT Abuja - Fitaccen lauyan nan mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Femi Falana, ya yi kira ga hukumar yan sandan farin kaya (DSS) ta gaggauta gama bincike kan Abdulrasheed Bawa da Godwin Emefiele.

Lauyan ya buƙaci DSS ta hanzarta gama bincike kan tuhumar da take wa dakataccen shugaban hukumar yaƙi da rashawa (EFCC) da dakataccen gwamnan CBN.

Haɗakar Hotunan Emefiele, Bawa da kuma Femi Falana.
Falana Ya Bukaci DSS Ta Hanzarta Bincike, Ta Gurfanar da Bawa da Emefiele a Kotu Hoto: channelstv
Asali: UGC

Channels tv ta rahoto cewa DSS ta yi ram da Emefiele jim kaɗan bayan dakatar da shi daga matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) bisa zargin hannu a angiza wa 'yan ta'adda kuɗi.

Kara karanta wannan

Wane Hukunci Aka Ɗauka Kan Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari? INEC Ta Fallasa Gaskiya

A ɗaya ɓangaren kuma hukumar ta titsiye Abdulrasheed Bawa bisa zargin aikata laifukan da suka shafi cin mutuncin ofishinsa na shugaban EFCC gabanin a dakatar da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Menene mataki na gaba bayan kammala bincike?

Da yake hira a cikin shirin 'Politics Today' Falana ya roƙi hukumar DSS ta gurfanar da mutanen biyu idan ta gano cewa suna da hannu a tuhume-tuhumen da ake masu.

Ya ƙara da cewa ci gaba da tsare Emefiele da Bawa ya saɓa wa kundin dokokin aikata manyan laifuka a Najeriya, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Babban lauyan wanda ya kai matsayin SAN ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tafiyar da Kes ɗin mutanen biyu bisa tsari da tanadin doka domin kauce wa faɗa wa wani laifin.

"Ya kamata a hanzarta gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake masu, ban yi tsammanin binciken muhimmin zargi zai ɗauki lokaci ba."

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Sarkin Musulmi Ya Faɗa Wa Yan Najeriya Abu 2 Da Ya Kamata Su Yi Wa Shugabanni

"Game da Emefiele, tun bara DSS take zargin yana da hannu a angiza wa yan ta'adda kudaɗe, dan Allah ku hanzarta yin abinda ya dace kan wannan. Game da halasta kuɗin haram kuma ya kamata a kai su inda ya dace."
"Dangane da kes din Bawa, har yanzu ba'a faɗa mana laifukan da ake zarginsa ba, ba zan ce komai ba illa kira ga FG ta gaggauta gama bincike, ta gurfanar da su gaban Kotu idan suna da laifi."

- Femi Falana.

Daga Karshe, Sultan Ya Goyi Bayan Shugaba Tinubu Game da Cire Tallafin Mai

A wani labarin na daban kuma Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar, ya tabbatar da goyon bayansa ga gwamnatin Bola Tinubu.

Sultan ya ce duk da al'umma sun shiga yanayin ƙunci da wahala, nan gaba zasu gane muhimmancin matakan da Tinubu ya ɗauka zuwaƁyanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262