Daga Karshe, Sultan Ya Goyi Bayan Shugaba Tinubu Game da Cire Tallafin Mai
- Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar, ya tabbatar da goyon bayansa ga gwamnatin Bola Tinubu
- Sultan ya ce duk da al'umma sun shiga yanayin ƙunci da wahala, nan gaba zasu gane muhimmancin matakan da Tinubu ya ɗauka zuwa yanzu
- Ya gode wa Kashim Shettima bisa kawo masa ziyarar barka da Sallah kana ya masa addu'ar fatan nasara a mulki
Sokoto state - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu gagarumin goyon bayan mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, game da matakan da ya ɗauka zuwa yanzu.
Sultan Abubakar na Sakkwato ya bayyana cewa yanzu ne ya kamata a ɗauki irin waɗan nan matakan duk ƙunci da wahalar da za'a shiga domin saita akalar ƙasar nan.
Sarkin Musulmin ya yi wannan furucin ne yayin da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya kai masa ziyarar barka da Sallah a fadarsa da ke Sakkwato.
Ya ce nan gaba 'yan Najeriya zasu ga alfanun waɗan nan matakan da gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗauka, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Basaraken ya ƙara da cewa ɗumbin alherin da 'yan Najeriya zasu gani shekaru masu zuwa sakamakon waɗan nan matakan da Tinubu ya ɗauka sun fi muhimmanci fiye da wahalhalun da ake sha yanzu.
Ya jaddada goyon bayan masarautarsa ta Sultan ga tsarukan gwamnatin tarayya da sabbin shirye-shirye, inda ya ce:
"Muna goyon bayanku 100 bisa 100, mun baku kalmarmu kuma zamu yi duk mai yuwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan."
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa daga cikin matakan da Tinubu ya ɗauka da suka jefa jama'a cikin wahalar rayuwa harda cire tallafin man fetur.
Sultan ya yi wa Shettima Addu'a
Daga karahe mai alfarma sarkin Musulmin ya miƙa godiya ga mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, bisa tasowa da kansa ya kawo masa ziyarar barka da Sallah.
Ya kuma yi masa Addu'ar Allah ya ba shi iko da kwarin guiwar sauke nauyin da aka ɗora masa a matsayin mutum lamba biyu a Najeriya, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Kashim Shettima Ya Ziyarci Sarkin Musulmi a Fadarsa, Ya Roki Goyon Bayan Arewa
A wani rahoton kun ji cewa mataimakin shugaban kasa ya roƙi shugabannin arewa su haɗa kai da gwamnatin Tinubu a kokarin samar da zaman lafiya.
Kashim Shettima ya ce gwamnatin Tinubu zata yi aiki da Sarakunan gargajiya wajen bunƙasa kasar nan bayan gano rawar da zasu iya taka wa.
Asali: Legit.ng