Kashim Shettima Ya Ziyarci Sarkin Musulmi a Fadarsa, Ya Roki Goyon Bayan Arewa
- Kashim Shettima ya kai ziyara ga mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III a fadarsa da ke birnin Shehu
- Mataimakin shugaban ƙasan ya roki masu faɗa a ji na arewa su taimaki gwamnatin Tinubu a kokarinta na kawo karshen matsalar tsaro
- Ya ce gwamnatin Tinubu zata yi aiki da Sarakunan gargajiya wajen bunƙasa kasar nan bayan gano rawar da zasu iya taka wa
Sokoto - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya roƙi shugabannin arewa su goyi bayan yunkurin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na dawo da zaman lafiya a yankin.
Shettima ya yi wannan roko ranar Alhamis a Sakkwato yayin da ya kai ziyarar barka da Sallah ga mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III a fadarsa.
Ya buƙaci shugabannin siyasa su haɗa kai wajen tunkarar kalubalen tsaro, talauci da kuma zaman komawa wajen ci gaba a arewa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
A wata sanarwa da hadimin midiya a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Olusola Abiola, ya fitar, an ji Shettima na cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ina rokon jagororinmu na siyasa su haɗa kai wuri ɗaya su tunkari kalubalen tsaro, talaucin da ya zama ƙarfen kafa da kuma rashin ci gaba a shiyyar arewa."
"Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya san damuwar 'yan arewa, matsalar tsaron da ta addabi Arewa maso Yamma, kuma yana ɗaukar matakai masu kyau domin dawo da zaman lafiya."
Shettima ya isar da sakon Tinubu ga Sarkin Musulmi
Haka zalika, Shettina ya isar da saƙon shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na barka da Sallah babba ga mai alfarma Sarkin Musulmai.
A rahoton Premium Times, mataimakin shugaban ƙasa ya kuma jaddada muhimmanci da amfanin zaman lafiya, inda aka ji yana cewa:
"Sai da zaman lafiya ake samun ci gaba kuma sai da ci gaba ake samun zaman lafiya."
Ya kara da bayanin cewa gwamnatin shugaba Tinubu ta fahimci rawar da Sarakuna ke takawa kuma a shirye take wajen ba su goyon baya domin ci gaban ƙasa.
Gwamna Aliyu Ya Fara Rabawa Nakasassu N6,500 Duk Wata
A wani rahoton kun ji cewa Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu ya cika alƙawarin da ya ɗauka na dawo wa tallafin da ake baiwa naƙasassu kowane wata N6,500.
Idan baku manta ba, a jawabinsa na ranar ranstuwar kama aiki, sabon gwamnan ya yi alƙawarin dawo da ɗan hasafin da gwamnati ke yi wa naƙasassu duk wata.
Asali: Legit.ng