Yanzu Yanzu: Shugaban NUC Ya Mika Mulki Ga Mataimakinsa Bisa Radin Kansa

Yanzu Yanzu: Shugaban NUC Ya Mika Mulki Ga Mataimakinsa Bisa Radin Kansa

  • Babban sakataren hukumar kula da jami'o'i a Najeriya (NUC), Farfesa Abubakar Rasheed, ya yi murabus daga kujerarsa
  • A ranar Juma'a, 30 ga watan Yuni, ya mika ragamar harkokin hukumar ga mataimakinsa, Chris Maiyaki, a hedkwatar hukumar
  • Wannan ci gaban na nufin Maiyaki zai yi aikin rikon kwarya har zuwa lokacin da gwamnatin tarayya za ta nada ainahin babban sakataren hukumar

FCT, Abuja - Farfesa Abubakar Rasheed, babban sakataren hukumar kula da jami'o'in Najeriya (NUC), ya sauka daga kujerarsa bisa radin kansa sannan ya mika ragamar kula da harkokin hukumar ga mataimakinsa, Chris Maiyaki.

An tabbatar da hakan ne a cikin wata wallafa da ya yadu a twitter da kuma hoton mika shugabancin a Abuja a ranar Juma'a, 30 ga watan Yuni.

Abubakar Rasheed
Yanzu Yanzu: Shugaban NUC Ya Mika Mulki Ga Mataimakinsa Bisa Radin Kansa
Asali: Facebook

Kafin mika shugabancin, Maiyaki ya kasance mataimakin babban sakataren hukumar ta NUC.

Kara karanta wannan

Mutane 6 Sun Rasu a Borno Yayin Da Wani Bam Da 'Yan Boko Haram Suka Binne a Kan Hanya Ya Tashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanzu Maiyaki zai yi aikin rikon kwarya a hukumar har zuwa lokacin da gwamnatin tarayya za ta nada ainahin babban sakataren hukumar.

Wannan kuma yana da alaka da duba abubuwan bukata da cike sharudda kafin gwamnatin tarayya ta yanke hukunci.

Hukumar kula da jami'o'i ta kasa hukuma ce ta gwamnati da ke tabbatar da samar da ingantaccen ilimin jami'a a Najeriya.

An kafa Hukumar wacce ke zamanta a Abuja a 1962 a matsayin hukumar bayar da shawarwari a ofishin majalisar ministoci.

A 1974, ta zama hukuma mai zaman kanta, kuma babban sakatarenta na farko shine Farfesa Jibril Aminu.

Shugaban hukumar NUC ya yi murabus daga kujerarsa

Da farko mun ji cewa Shugaban hukumar NUC mai kula da jami’o’i a Najeriya, Abubakar Adamu Rasheed ya sauka daga matsayin da yake kai a yanzu.

Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya sanar da cewa ya rubuta murabus da kan shi domin barin matsayin da ya yi shekaru har bakwai a kai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

Ya shaidawa manema labarai wannan ranar Litinin a Abuja, ya nuna kwanakinsa sun zo karshe.

Sanata Shehu Sani ya shawarci Tinubu da ya binciki gwamnatin baya

A wani labari na daban, Sanata Shehu Sani ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi watsi da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari sannan ya binciki jami'an gwamnatin baya.

Sani ya ce ya zama wajibi Tinubu ya kwato kudaden da aka wawure idan ba haka ba kudaden da aka sace za su farauto shi ko ba jima ko ba dade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng