“Ka Share Buhari, Ka Binciki Gwamnatin Baya” – Shehu Sani Ga Tinubu
- Tsohon dan majalisa Shehu Sani ya bayyana abun da ya zama dole shugaban kasa Bola Tinubu ya yi domin yin nasara a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16
- Sani ya bukaci shugaban kasa Tinubu da kada ya bata lokaci a yunkurinsa na bincikar jami'an gwamnatin baya da dawo da kudaden da aka sace
- Dan fafutukar ya bayyana cewa idan Tinubu ya ki kwato kudaden da aka sace, su za su farauto shi ko ba jima ko ba dade
Tsohon sanata da ya wakilci Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya aika gagarumin sako ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Sani ya bukaci Tinubu da ya gaggauta fara binciken ayyukan jami'an gwamnatin baya wadanda suka yi aiki karkashin gwamnatin baya karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Abun da ya kamata Tinubu ya yi wa tsoffin ministoci, Shehu Sani ya bayyana
Dan siyasar ya bayyana hakan ne a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sani ya bukaci Tinubu da ya yi watsi da Buhari sannan ya ci gaba da kwato kudaden da aka wawure saboda kada abubuwa su tabarbare a gwamnatinsa.
"Ya kamata Tinubu ya yi watsi da Buhari sannan ya ci gaba da binciken gwamnatin baya da kwato kudaden da aka wuware. Idan shugaban kasa Tinubu ya ki bibiyar kudaden da aka sace, kudaden da aka wawure za su farauto shi ko ba jima ko ba dade," inji Sani.
Shehu Sani ya bayyana dalilin da yasa ya kamata Tinubu ya binciki Buhari, tsoffin ministoci, tsoffin shugabannin tsaro da sauransu
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilin da ya sa akwai bukatar shugaban kasa Bola Tinubu ya binciki tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ministocinsa, da tsoffin shugabannin tsaro na gwamnatinsa.
Yanzu Yanzu: Buhari Ya Bukaci Tinubu Ya Dakatar Da Binciken Emefiele Da Sauransu? Gaskiya Ta Bayyana
Sani ya bayyana cewa ya kamata Tinubu ya binciki laifuka na tattalin arziki da aka aikata a gwamnatin Buhari.
A cewar Sani, sauya fasalin kudin kasar ba shi kadai ne aika-aikar da aka yi a gwamnatin ba kuma kada mutum daya ko biyu ba zai samar da amsoshin da ake bukata ba.
Asali: Legit.ng