Ana Rade-Radi Gwamna Ya Mutu a Asibitin Waje, Jam’iyya da Gwamnati Sun Yi Magana
- Jita-jita sun fara yawo a gari cewa Gwamnan jihar Ondo ya mutu a wajen neman magani a kasar waje
- Gwamnan rikon kwarya, Lucky Ayedatiwa ya yi magana kan rade-radin mutuwar Rotimi Akeredolu
- Tsohon abokin adawar Gwamnan na APC, Olusola Oke ya ce Akeredolu ya na samun lafiya a asibiti
Ondo - Gwamnan rikon kwarya na jihar Ondo, Lucky Ayedatiwa, ya yi kira ga al’umma su yi amfani da lokacin sallah wajen yi wa Rotimi Akeredolu addu’a.
Vanguard ta ce a sakon barka da sallah da ya fitar a jiya, Mista Lucky Ayedatiwa ya bukaci mazauna jihar su yi addu’a Ubangiji ya ba Rotimi Akeredolu lafiya.
Mu yi amfani da wannan lokaci na musamman wajen yi wa gwamnatin nan addu’ar samun nasara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kuma mu roki Ubangihi ya ba Gwamna Rotimi Akeredolu karfin lafiyar cigaba da yi wa jiharmu aikin kwaran da yake yi.
Ayedatiwa ya tabbatar da cewa gwamnainsu za su cigaba da bakinkokarinsu wajen tabbatar da tsaro, zaman lafiya da cigaban jihar Ondo a kowane bangare.
The Cable kuwa ta rahoto Olusola Oke ya na cewa Rotimi Akeredolu ya na samun sauki sosai a asibiti, hakan martani ga masu yada munanan jita-jita a jihar.
Tsohon ‘dan takaran Gwamnan ya bayyana masu yawo da labaran karya na mutuwar Mai girma Akeredolu a matsayin mugaye kuma wadanda su da imani.
A matsayinmu na ‘dan Adam, Oke ya ce kowa ya na iya kwantawa rashin lafiya, har ta kai a nemi magani, kuma ayi jinya, ya ce gwamna ya na samun lafiya.
Kamar yadda aka bukata, jaridar ta rahoto ‘dan siyasar ya na cewa mutane su na yi wa shugaban na su addu’o’i Ubangiji ya dawo da shi cikin koshin lafiya.
Za a cafke makaryata - APC
Ita kuwa APC ta yi kaca-kaca da masu yawo da jita-jitar mutuwar Gwamna Akeredolu, jam’iyyar ta ce akwai bukatar a cafke masu aika-aikar nan.
Shugaban jam’iyya na reshen Ondo, Ade Adetimehin ya ce labaran da ake yadawa ya na damunsu, idan aka kama masu laifi, za a kai su wajen ‘yan sanda.
Asali: Legit.ng