Muna Dab da Hukunta Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa, INEC

Muna Dab da Hukunta Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa, INEC

  • Hukumar INEC ta ce nan ba da jimawa ba zata ɗauki mataki kan dakataccen kwamishinan zaɓen jihar Adamawa
  • Festus Okoye, kwamishinan yaɗa labarai na INEC ya ce suna da masaniyar cewa hukumar 'yan sanda ta gama bincikar Hudu Ari
  • Barista Hudu Ari ya tada ƙura a Najeriya bayan ya ayyana Aishatu Binani a matsayin wacce ta ci zaben gwamna a Adamawa

FCT Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba zata ɗauki mataki kan dakataccen kwamishinan zaɓen Adamawa, Hudu Ari.

Kwamishinan yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa kuri'a na INEC ta ƙasa, Festus Okoye ne ya faɗi haka yayin hira a shirin siyasa a yau na Channels tv.

Kwamishinan yaɗa labaran INEC, Festus Okoye.
Muna Dab da Hukunta Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa, INEC Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Idan zaku iya tunawa, Mista Ari ya haddasa ruɗani da cece-kuci lokacin da ya ayyana sakamakon cikon zaɓen gwamnan Adamawa tun kafin gama tattara sakamako.

Kara karanta wannan

CAN Ta Ja Hankali, Ta Yi Magana Kan Mahaucin da Aka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW a Sakkwato

Ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta jam'iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben a wancan lokacin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan faruwar haka, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya umarci a gudanar da bincike mai zurfi kan jami'an tsaron da ke da hannu a lamarin wanda ya saɓa wa doka.

Yaushe za'a hukunta Barista Hudu Ari?

Yayin wannan hira, Mista Okoye ya ce:

"Game da batun kwamishinan zaɓen Adamawa (REC) kun san cewa shugaba Buhari ya dakatar da shi tun kafin sauka daga mulki kuma 'yan sanda sun gayyace shi domin ya yi bayanin abinda ya faru."
"Mun samu labarin hukumar 'yan sanda ta gama bincike kuma nan da makonni kalilan zamu sanar da 'yan Najeriya abinda ya faru."
"Mun zauna mun tattauna tsakanin yan sandan Najeriya da INEC, an gaya wa hukumar zaɓe wasu matakai da aka ɗauka. Nan ba da jimawa ba INEC zata ɗauki mataki kan REC ɗin."

Kara karanta wannan

Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya

Ganduje Ya Koka Kan Matakin Abba Gida Gida Na Dakatar da Albashin Ma'aikata 10,000

A wani labarin na daban kuma Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya nuna damuwa kan matakin dakatar da albashin ma'aikata sama da 10,000 a jihar Kano.

Ganduje ya ce wannan wani yunkuri ne da ke nuna mafufar sabuwar gwamnatin Abba Kabir Yusuf na korar ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262