“Bana Biyan Kudin Haya a Lagas”: Budurwa Ta Baje Kolin Gidanta Na N250m, Yana Da Katon Kicin

“Bana Biyan Kudin Haya a Lagas”: Budurwa Ta Baje Kolin Gidanta Na N250m, Yana Da Katon Kicin

  • Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta nuna cikin gidanta da ya kai miliyan N250 a Lekki
  • Matashiyar ta bayyana cewa komai ya ji a gidan mai dakuna hudu, kuma babu abun da bata so a gidan
  • Mai gidan ta nuna bandakin da ke cikin dakinta da katon farandar da ke hade da wajen don shakatawa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani shahararren mai watsa shirye-shirye, Wales Morgan, ya cika da mamaki lokacin da ya tunkari wata matashiyar budurwa a Lagas sannan ya tambayi nawa take biya kudin hayar gidanta a jihar.

Matashiyar ta fada mai cewa ta mallaki gidan kanta da ya kai naira miliyan 250 a jihar sannan ta zagaya da Morgan cikin gidan don nuna masa yadda yake.

Budurwar ta ce tana son komai na gidan
“Bana Biyan Kudin Haya a Lagas”: Budurwa Ta Baje Kolin Gidanta Na N250m, Yana Da Katon Kicin Hoto: @walesmorgan
Asali: TikTok

Hadadden gida na gani na fada

Komai na gidan mai dakuna 4 da ke yankin Lekki ya hadu iya haduwa. Fitiloli da komai da aka kawata gidan da shi tsadaddu ne.

Kara karanta wannan

Aji Ya Fadi: Santaleliyar Budurwa Ta Rufe Fuskarta Don Kunya Bayan Kawayenta Sun Gano Tana Gadi a Otal

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da take bayyana tushen arzikinta, matashiyar ta ce tana aikin gine-gine da kawata cikin gida ne.

Matashiyar ta ce tana da hanyoyin lantarki masu amfani da hasken rana don tabbatar da samun wutar lantarki kodayaushe. Dakin baccinta na da wajen wanka da hadadden faranda.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Queen dkd ta ce:

"Miliyan 250 amma gida na kama da 2017."

EMMY SOFT ya ce:

"250M kan wannan karamin gidan na mutu."

SUSU_BABŸ ta ce:

"Cikin komai labulayen ne suka bani haushi..."

Ajao Saheed Cdorf ya ce:

"250 m ya yi yawa kan gidan koda dai gidan na da kyau amma gaba daya 70m."

Bad_Captain05 ya ce:

"Komai ya yi sai dai labulen."

princedrsamueloluomo ta ce:

"Ki barmu mu talakawa mu numfasa. Kada ki shagure mu don Allah."

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: CAN Ta Taya Musulmai Murnar Bikin Layya, Ta Nemi A Yi Addu'o'i Don Zaman Lafiya

Matashiya ta fashe da kuka bayan ta bude dilar gwanjo da ta siya N250k, duk tarkace ne a ciki

A wani labarin kuma, wata matashiya da ke sana'ar siyar da gwanjo ta tsinci kanta a wani yanayi bayan ta siya dil;ar gwanjo kan N250k.

Koda matashiyar ta bude kayan sai ta ga kwata-kwata bai yi darajar kudin ba hasalima, duk tarkace ne a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng