Babban Sallah: Gwamnan Jihar Gombe Ya Kara Hutun Sallah Har Zuwa Ranar Juma'a

Babban Sallah: Gwamnan Jihar Gombe Ya Kara Hutun Sallah Har Zuwa Ranar Juma'a

  • Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana ranar Juma'a, 30 ga watan Yunin 2023 a matsayin ranar hutu a jiharsa
  • Kamar yadda gwamnatin Gombe ta sanar, an bayar da hutun ranar Juma’an ne domin ci gaba da shagulgulan babbar Sallah
  • Ana sanya ran ma'aikatan jihar za su koma bakin aiki a ranar Litinin, 3 ga watan Yuli kamar yadda sanarwar ta bayyana

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi umurnin tsawaita hutun babbar sallah har zuwa Juma'a, 30 ga watan Yuni, jaridar Punch ta rahoto.

Gwamna Inuwa Yahaya
Babban Sallah: Gwamnan Jihar Gombe Ya Kara Hutun Sallah Har Zuwa Ranar Juma'a Hoto: Punch
Asali: Twitter

An karawa ma'aikata hutu har zuwa ranar Juma'a don ci gaba da shagulgulan sallah babba

A cewar wata sanarwa da Jibrin Yusuf ya saki a madadin mukaddashin shugaban ma'aikatan gwamnati na jihar Gombe, Ahmed Abdullahi, a ranar Alhamis, ya ce an kara hutun ne domin tabbatar da ganin ma'aikata sun ji dadin bukukuwan tare da takwarorinsu na duniya.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Jihar Kano Daga Sake Cafke Doguwa Bisa Zargin Kisan Kai

Sanarwar ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"An umurceni na sanar da ku cewa mai girma gwamna, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, (Dan Majen Gombe) ya amince da kara wa'adin hutu zuwa ranar Juma'a 30 ga watan Yunin 2023 domin ma'aikatan gwamnati a jihar su ci gaba da shagalinsu na babban sallan bana tare da takwarorinsu na duniya."

Yayin da yake masu fatan dawowa cikin farin ciki a ranar Litinin, ya karra da cewar za a ci gaba da gudanar da muhimman ayyuka.

Yusuf ya kara da cewar:

"Mukaddashin shugaban ma'aikatan gwamnati na yiwa daukacin ma'aikata da jama'a baki daya fatan bikin sallah cikin kwanciyar hankali.
"A halin da ake ciki, za a ci gaba da gudanar da duk wasu ayyuka masu muhinmmanci a tsawon hutun sannan ma'aikata za su dawo bakin aiki a ranar Litinin 3 ga watan Yuli, 2023, don Allah."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

Babbar Sallah: Peter Obi ya nauki nauyin gyara masallatai

A wani labari na daban, mun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar LP, Peter Obi, ya gana da shugabannin Musulmai a gidansa da ke garin Onitshan jihar Anambra.

Obi dai ya gayyaci musulman gidansa ne domin ya taya su murnar babbar sallah inda har ya bayar da gudunmawar kudi domin gyara masallatai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng