Rusau a Kano: 'Yan Kasuwa Sun Koma Ga Allah Sun Nemi Ya Kawo Musu Mafita

Rusau a Kano: 'Yan Kasuwa Sun Koma Ga Allah Sun Nemi Ya Kawo Musu Mafita

  • Ƴan kasuwan da rusau ɗin gwamnan jihar Kano, Abba Gida-Gida ya ritsa da su sun gudanar da Sallar nafila domin neman mafita a wajen Allah
  • Ƴan kasuwar sun koka kan halin da suka tsinci kan su a ciki bayan rushe musu wuraren neman na abincinsu
  • Gwamnatin jihar dai tace tana rusau ɗin ne domin wuraren kadarorin gwamnati ne waɗanda aka rabar ba bisa ƙa'ida ba

Jihar Kano - Ƴan kasuwan da aka rushewa shaguna a filin Idi na Kofar Mata a jihar Kano, sun gudanar da Sallah ta musamman domin neman ɗauki daga wajen Allah.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa, ƴan kasuwan bayan sun gabatar da Sallar Nafila raka'a biyu, sun roƙi Allah ya kawo musu mafita

Yan kasuwa sun gudanar da Sallah kan rusau a Kano
Wani waje wanda aka rushe a Kano Hoto: Aminiya.com
Asali: UGC

Sun zargi gwamnatin jihar da yin rusau ɗin ba bisa ƙa'ida ba da rashin duba halin da masu shagunan da basu ji ba basu gani ba za su shiga.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mummunar Gobara Ta Tashi a Gidan Shugaban Kungiyar Kwadago Ta Kasa, An Tafka Gagarumar Asara

Ƴan kasuwan sun shiga halin ƙunci a dalilin rusau

Ƴan kasuwan sun koka da cewa basu san hawa ba basu san sauka ba sai dai kawai aka kama rushe musu shaguna domin ba a sanar da su cewa za a yi rusau ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani ɗan kasuwa, Muhammad Sadiq, ya bayyana cewa rusau ɗin ya sanya su cikin halin ƙunci wanda za su daɗe basu warke daga shi ba.

Gwamnatin jihar Kano a ƙoƙarin dawo da martabar birnin Kano da ƙwato kadarorin gwamnati, ta rushe gine-ginen da ta kira haramtattu ne waɗanda kuɗinsu ya kai biliyoyin naira.

Duk da cewa gwamnatin ta yi nuni da cewa akwai alheri a cikin rusau ɗin, ƴan kasuwar da lamarin ya ritsa da su sun yi amanna cewa hakan ya ruguje kasuwancin mutane da dama da janyo mutane da dama sun koma marasa ayyukan yi a jihar.

Kara karanta wannan

Shagalin Sallah: Gwamnan Arewa Ya Biya Tarar Miliyan N20m, An Saki Fursunoni 80 Daga Kurkuku

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za ta kafa wani kwamiti wanda zai duba koken masu gine-ginen da rusau ɗin ya ritsa da su domin kwato kadarorin gwamnati.

Peter Obi Ya Sanya Baki a Rusau Din Kano

A wani labarin na daban kuma, kun ji ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi magana kan rusau ɗin da gwamnatin Abba Gida-Gida ke yi a jihar Kano.

Peter Obi ya bayyana cewa wasu rushe-rushe da gwamnatin Kano ke yi za a iya kauce musu da kuma yin uzuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel