Fulani Sun Nemi Shugaba Tinubu Ya Tuna Da Su, Sun Aike Da Muhimmiyar Bukata 1
- Fulani makiyaya sun yunƙuro inda suka aike da muhimmiyar buƙata zuwa ga gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Wata ƙungiyar Fulani makiyaya ta Kulen Allah Cattle Rearers Association of Nigeria (KACRAN) ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya riƙa tunawa da makiyaya a gwamnatinsa
- Ƙungiyar ta yi kiran da a riƙa ware kaso mai tsoka a cikin kasafin kuɗi domin bunƙasa ɓangaren kiwon dabbobi a ƙasar nan
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Wata ƙungiyar Fulani makiyaya mai suna Kulen Allah Cattle Rearers Association of Nigeria (KACRAN), ta aike da buƙatunta ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ƙungiyar ta KACRAN ta buƙaci shugaba Tinubu da ya kawo ƙarshen rashin saka makiyaya da ake yi a cikin tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnati duk lokacin da hakan ya taso, jaridar Daily Trust ta yi rahoto.
Kungiyar ta KACRAN ta yi nuni da cewa ana mantawa da Fulani makiyaya idan tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnati sun taso a ƙasar nan, wanda a cewarta hakan yakamata ya zo ƙarshe.
Ƙungiyar KACRAN ta aike da buƙatunta ga gwamnatin Shugaba Tinubu
Ƙungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, 27 ga watan Yunin 2023 wacce shugabanta, Khalil Mohd Bello, ƴa rattaɓawa hannu, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta riƙa ware kuɗi domin haɓɓaka ɓangaren kiwon dabbobi na ƙasar nan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ƙungiyar ta nemi gwamnatin tarayya da ta riƙa ware kaso mai tsoka a cikin kasafin kuɗi domin bunƙasa ɓangaren kiwon dabbobi a Najeriya.
Ƙungiyar ta kuma miƙa ƙoƙon baranta a wajen gwamnatin tarayyar kan ta riƙa bayar da tallafi ga makiyayan ƙasar nan domin su ma su riƙa amfana da gwamnati.
Da Dumi-Dumi: Mummunar Gobara Ta Tashi a Gidan Shugaban Kungiyar Kwadago Ta Kasa, An Tafka Gagarumar Asara
Gwamnatin Tinubu Za Ta Samar Da Ayyuka Miliyan 1 Ga Matasa
A wani labarin na daban kuma, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi bayanin cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi tanadi na musamman domin matasan ƙasar nan.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya yi bayani kan shirin gwamnatin tarayya na samar da ayyukan yi miliyan daya a bangaren fasahohin zamani domin bunƙasa ci gabansu.
Asali: Legit.ng