'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 5 a Wani Kauye a Jihar Plateau
- Ƴan bindiga sun sake kai mummunan farmaki a wasu ƙauyukan jihar Plateau a yankin Arewa maso tsakiya na Najeriya
- Miyagun ƴan bindingan sun halaka mutum biyar a yayin harin da suka kai ciki har da matar aure tare da mijinta
- Ƴan bindigan na ci gaba da cin karensu babu babbaka a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar duk kuwa da dokar ta ɓacin da gwamnatin jihar ta sanya a yankin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Plateau - Aƙalla mutum bakwai suka halaka bayan ƴan bindiga sun nao hari a ƙauyen Kerang cikin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.
Harin ya auku a ƙauyen ne duk da donar ta ɓaci ta sa'o'i 24 da gwamnatin jihar ta sanya a ƙaramar hukumar biyo bayan hare-haren da ƴan bindiga suka kai a ƙauyuka da dama satin da ya wuce, cewar rahoton The Punch.
Da Dumi-Dumi: Mummunar Gobara Ta Tashi a Gidan Shugaban Kungiyar Kwadago Ta Kasa, An Tafka Gagarumar Asara
A wani mazaunin ƙauyen na Kerang, Joseph Kabir, wanda ya tabbatar da aukuwar harin a ranar a ranar Talata, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka halaka akwai wani magidanci da matarsa.
Ya ƙara da cewa an binne waɗanda suka rasa rayukansu a harin da safiyar ranar Talata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
"Ina bayar da tabbacin cewa mutum biyar ciki har da wani magidanci da matarsa ƴan bindigan suka halaka daga ƙarfe 5:00 zuwa 8:00 na dare a ranar 26 a watan Yuni a ƙauyen Sohon Kerang cikin ƙaramar hukumar Mangu."
"Mun ɗauka cewa da dokar ta ɓacin da gwamnati ta sanya, jami'an tsaro za su hana ƴan bindigan halaka mutanen da basu ji ba basu gani ba."
"Amma ƴan bindigan sun shigo ƙauyen wanda yake a bayan kamfani ruwan SWAN da ke a ƙauyen Kerang da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, sannan suka kama harbe-harbe waɗanda suka yi siƙar mutuwar mutum biyar."
'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Kauyukan Jihar Bauchi
A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun kai farmaki a wasu ƙauyukan da ke a ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.
Ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutum huɗu yayin da mutanen yankin ke ci gaba da zaman ɗar-ɗar a dalilin ƙaruwar ayyukan ƴan bindigan a yankin.
Asali: Legit.ng