An Shiga Jimami Bayan Babban Kwamandan Hukumar Tsaro a Jihar Ogun Ya Kwanta Dama
- An shiga jimami a jihar Ogun bayan babban kwamandan hukumar tsaron jihar (Amotekun) ya koma ga mahaliccinsa
- CP David Akinremi wanda tsohon kwamishinan ƴan sanda ne ya yi bankwana da duniyar nan ne a yammacin ranar Litinin
- Babban kwamandan na Amotekun a jihar ya yi bankwana da duniya ne bayan ya kwashe lokaci mai tsawo yana fama da rashin lafiya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ogun - Kwamandan hukumar tsaro ta jihar Ogun, (Amotekun), CP David Akinremi (mai ritaya) ya yi bankwana da duniya.
Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa shugaban hukumar tsaron ya mutu ne a ranar Litinin, bayan ya yi fama da jinyar wata cuta wacce ba a bayyana sunanta ba.
A shekarar 2021 ne gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya naɗa shi a matsayin kwamandan hukumar tsaron ta Amotekun, bayan an kafa ta.
Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya
Kwamandan hukumar tsaron jihar mai suna So-Safe Corps (wata takwarar hukumar tsaro ta Amotekun), Soji Ganzallo, shi ne ya tabbatar da mutuwar Akinremi a ranar Talata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ganzallo ya bayyana mutuwar Akinremi a matsayin babban abu wanda ya yi matuƙar girgiza shi, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Ya daɗe yana fama da jinya
Akinremi wanda tsohon kwamishinan ƴan sanda ne ya daɗe yana jinya wacce daga ƙarshe ta zama ajalinsa.
A ƙarƙashin kulawarsa hukumar tsaron ta Amotekun ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro a jihar, domin kawar da ɓata gari masu aikata laifuka a jihar.
Gwamnonin yankin Kudu maso Yamma na ƙasar nan ne dai suka haɗa hannu waje ɗaya suka samar da hukumar tsaron ta Amotekun domin magance matsalae tsaro a yankunansu.
Tun bayan kafa hukumar a yankin na Kudu maso Yamma wanda ya haɗa da jihohin Legas, Ogun, Osun, Ekiti da Oyo, hukumar ta Amotekun ta shige gaba wajen magance matsalar tsaro a yankin.
Babban Farfesa a Jami'ar Jihar Legas Ya Mutu
A wani labarin na daban kuma, wani babban Farfesa a fannin koyar da aikin jarida a jami'ar jihar Legas, ya koma ga mahaliccinsa a wani mummunan hatsarin mota.
Farfesa Lai Oso wanda ake jo da shi a fannin koyar da aikin jarida a ƙasar nan, ya mutu ya bar duniya yana da shekara 67.
Asali: Legit.ng