Gwamna Bago Ya Biya Miliyan N20m Domin Sako Fursunoni 80 a Jihar Neja
- Gwamna Muhammad Bago na jihar Neja ya ceci Fursunoni 80 daga jidajen gyaran hali daban-daban ranar Litinin
- Bago, ya roƙi waɗanda suka shaƙi iskar 'yanci su yi amfani da wannan damar wajen aikata ayyuka nagari maimakon laifin da ka iya dawo da su gidan yari
- Gwamnatin Neja ta biya naira miliyan N20m a matsayin kuɗin tarar da ke kan Fursunonin guda 80
Niger State - Gwamnatin jihar Neja karkashin jagorancin gwamna Muhammed Bago ta biya tarar naira miliyan N20m domin ceto fursunoni 80 daga gidajen gyaran hali 8 da ke faɗin jihar.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa gwamnatin ta ji ƙan Fursunonin ne a wani yunkuri na rage cinkoson gidajen yari.
Gwamna Bago na jam'iyyar APC ya tabbatar da haka a wani ɗan kwarya-kwaryan bikin da aka shirya wa Fursunonin a gidan yarin Minna, babban birnin jihar Neja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Muhammed Bago ya ce waɗan da suka kuɓuta daga gidan yarin duk matasa ne masu ƙananan shekaru kuma da yawansu sun shiga gidan gyaran hali ne a karon farko kan ɗan ƙaramin laifi.
Bago, wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamna, Kwamaret Yakubu Garba, ya roƙi Fursunonin da suka samu 'yanci su guji aikata duk wani aiki da zai sa a sake dawo da su gidan Yari.
Bugu da ƙari gwamnan Bago ya ƙara rokon waɗanda suka samu yanci da su koma aikata ayyuka nagari da halastattu waɗanda zasu amfane su maimakon aikata abinda zai iya maida su gidan yari.
Sakin fursunonin ya yi daidai da kundin dokar ƙasa
Babbar Sakatariyar ma'aikatar harkokin siyasa ta jihar Neja, Hajiya Aishatu Usman ta ce sakin fursunonin ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya 1999 da aka yi wa garambawul.
Haka zalika kwanturolan hukumar kula da gidajen gyaran hali reshen jihar Neja, Salman Abdulkadir, ya ce hukumar ta karɓi naira miliyan N20n a matsayin tarar fursunonin.
Jirgin NAF Ya Yi Luguden Wuta Kan Mafakar 'Yan Ta'adda 3 a Arewa, Rayuka Sun Salwanta
A wani labarin na daban kuman Sojin saman Najeriya (NAF) sun yi luguden bama-bamai kan mafakar 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno.
Rahoto ya nuna cewa luguden wutan NAF ya halaka mayaƙan ISWAP da yawan gaske kuma ya yi kaca-kaca da wuraren da suke samun mafaka.
Asali: Legit.ng