Malam Nuhu Ribaɗu Ya Fara Aiki a Matsayin Mai Bada Shawara Kan Tsaro
- Sabon mai bada shawara kan tsaron ƙasa da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa ya kama aiki ranar Litinin
- Nuhu Ribaɗu ya karbi ragamar ofishin NSA daga hannun Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya a birnin tarayya Abuja
- A jawabinsa, ya ce zai yi iya bakin kokarinsa wajen inganta tsaro da ceto Najeriya daga halin da ta shiga
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Malam Nuhu Ribaɗu ya fara aiki a matsayin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron kasa (NSA) ranar Litinin, 26 ga watan Yuni, 2023.
Daily Trust ta rahoto cewa Ribadu ya shiga ofishinsa bayan tsohon NSA, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya ya miƙa masa ragamar aiki yau Litinin.
Zan yi iya bakin kokarina domin dawo da tsaro - Ribadu
Da yake jawabi bayan karɓan ragama, Malam Ribaɗu ya ce zai yi amfani da duk wata kwarewa da basirar da Allah ya ba shi wajen magance matsalar tsaro da saita Najeriya.
Babban Rashi: Allah Ya Yi Wa Fitaccen Ɗan Siyasa Kuma Makusancin Atiku Abukar Rasuwa, Bayanai Sun Fito
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na da jan aiki a gabanta na ceto Najeriya da kuma tabbatar da tsaro a kowane ɓangaren ƙasar nan.
A cewarsa, wannan aiki ne da nauyin 'yan Najeriya kuma ya shirya tsaf ɗomin ɗorawa kan abinda aka aiwatar masu kyau a baya.
A rahoton The Nation, Sabon NSA ya ce:
"Zamu daidaita Najeriya, zamu ceto ƙasar nan kuma zamu dawo da zaman lafiya a Najeriya saboda mun yi imanin cewa lokaci ya yi da ƙasarmu zata zauna lafiya, a ci gaba da bin doka da oda kamar sauran kasashen duniya."
"Gyara ƙasa wani aiki ne da dole sai an bi matakai a hankali da hankali, zamu kalli abinda aka yi a baya domin mu ɗora daga nan. Muna buƙatar goyon bayanku a kokarin sauke nauyin da ke kanmu."
"Mai girma shugaban kasa na da jan aikin gyara da tsare kowane lungu da saƙo na ƙasar nan kuma zamu yi aiki da masu ruwa da tsaki don tabbatar da wannan manufa."
An Gano Gwarwakin Ɗaliban Jami'ar Ahmadu Bello Zariya Bayan Awanni 48
A wani rahoton kuma Bayan kwana biyu da haɗari, an samu nasarar ciro gawarwakin ɗaliban jami'ar ABU da suka nutse a ruwa a Kalaba, babban birnin Kuros Riba.
Kwamishinan yan sandan Kuros Riba ya tabbatar da cewa mutanen gari sun ba da gudummuwa mai girma yayin aikin ceto.
Asali: Legit.ng