Hadarin Jirgin Ruwa: Bayan Kwana 2, An Gano Gawarwakin Ɗaliban ABU a Kalaba

Hadarin Jirgin Ruwa: Bayan Kwana 2, An Gano Gawarwakin Ɗaliban ABU a Kalaba

  • Bayan kwana biyu da haɗari, an samu nasarar ciro gawarwakin ɗaliban jami'ar ABU da suka nutse a ruwa a Kalaba, babban birnin Kuros Riba
  • Tun ranar Asabar, jirgin ruwan da ya ɗauko ɗaliban likitanci 14 ya kife a cikin ruwa kuma a ranar aka ceto 11 daga ciki
  • Kwamishinan yan sandan Kuros Riba ya tabbatar da cewa mutanen gari sun ba da gudummuwa mai girma yayin aikin ceto

Cross River - Awanni 48 bayan jirgin ruwan da ya ɗauko ɗaliban da ke koyon aikin Likitanci ya kife a Tekun Kalaba, jihar Kuros Riba, an gano gawar ragowar mutum uku da suka ɓace.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa tun bayan haɗarin jirgin, masu kai agaji suka yi nasarar ceto 11 daga cikin ɗalibai 14 da jirgin ya kwaso, yanzu an gano gawar sauran guda 3.

Kara karanta wannan

Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya

Daliban ABU da suka rasu a Kalaba.
Hadarin Jirgin Ruwa: Bayan Kwana 2, An Gano Gawarwakin Ɗaliban ABU a Kalaba Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa mutanen yankin da suka iya ruwa sun ci gaba da lalube har zuwa yammacin Lahadi lokacin da su ke tsammanin wurin da za'a iya ganin ragowar ɗaliban awanni 24 bayan sun nutse.

Sai dai ba su samu nasarar tsamo su ba tun da yammacin Lahadi har sai da safiyar Litinin din nan, 26 ga watan Yuni, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin gawarwakin uku da aka tsamo yau biyu ɗaliban Likitanci ne a jami'ar Ahmadu Bello Zariya, (ABU), Mustapha Aminu Tukur da kuma Kabiru Hamza.

Kwamishinan 'yan sanda ya yi ƙarin haske

The Nation ta ce da yake hira da 'yan jarida a bakin ruwan Kalaba, kwamishinan 'yan sandan jihar Kuros Riba, Gyogon Augustine Grimah, ya yi bayanin cewa:

"Lokacin da haɗarin ya faru, 'yan sandan bakin ruwa sun kai ɗaukin gaggawa tare da agajin mutanen da suka iya ruwa kuma an samu nasarar ciro gawarwakin."

Kara karanta wannan

Shagalin Sallah: Gwamnan Arewa Ya Biya Tarar Miliyan N20m, An Saki Fursunoni 80 Daga Kurkuku

"Ɗalibai uku ne suka ɓata kuma tun wannan lokacin bamu huta ba, haka muka ci gaba da lalubensu har zuwa yau da muka zo nan domin sanar da ku mun ciro sauran."
"Mutanen gari sun yi namijin kokari kuma a halin yanzu sun kawo mana gawarwakin ragowar ɗaliban guda uku."

Lamarin ya girgiza mu - NiMSA-ABU

Legit.ng Hausa ta tuntubi shugaban ƙungiyar ɗalibai likitoci reshen ABU, Kwamaret Umar Kareto, ya ce lamarin ya girgiza ɗalibai musamman mambobin NiMSA.

Ya shaida wa wakilinmu cewa ɗaliban da sauran wakilan ƙungiyar NiMASA daga rassa daban-daban sun je Kalaba ne domin halartar taron, "Makon lafiya" wanda aka saba shirya wa duk shekara.

Kwamaret Umar ya ce a tsarin makon lafiya na bana an ware ranar Asabar domin fita rangadi da yawon buɗe ido domin ɗalibai su ɗan fita ganin wurare.

A kalamansa ya ce:

"Da fari sun fara zuwa gidan aje kayan tarihi wanda ke kusa da wajen hutawa na gabatar Teku, bayan sun fito suka ƙarisa suka shiga kwale-kwale su 14, ɗaliban mu na ABU 2 suna ciki."

Kara karanta wannan

NSA: Sabon Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaron Kasa Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

"An ce an basu rigar kariya kuma tabbas sun ɗora a shafukan sada zumunta, to bayan sun fara tafiya a ruwa bai wuce 200 mita ba sai jirgin ya fara tangal-tangal, ashe ba bu isasshen mai kuma tankin na zuba."
"Haka nan ba su da masu kai agaji cikin hanzari, rigunan da aka basu duk ba su aiki, sai da aka kira sojojin ruwa kuma da suka zo sun samu nasarar ceto ɗalibai 11 da kusan karfe 3:00 na yammacin Asabar."

Umar ya ƙara da cewa ɗaliban ABU 2 na cikin ragowar mutun uku da ba'a ceto ba a wannan lokacin, ragowar ɗayar wata ɗaliba ce daga jihar Oyo.

"Tun ranar Asabar ba'a gano su ba sai da safiyar ranar Litinin, kuma an so dawo da su gida domin a musu Janaza amma yanayin gawar kwana 3 a ruwa ya sa a can aka musu jana'iza."

Dangane da matakin da NiMASA zata ɗauka kuma, Kwamaret Umar ya ce suna kan tattaunawa amma bisa la'akari da gangancin masu wurin, ƙungiyar na tunanin kai ƙara Kotu.

Kara karanta wannan

Kan Abu 1, Abba Gida Gida Ya Dakatar da Albashin Ma'aikata Sama Da 10,000 a Jihar Kano

Fitaccen Ɗan Siyasa Kuma Makusancin Atiku Abubakar Ya Rasu a Abuja

A wani labarin kuma Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Maiha da ya gabata a Adamawa, Idi Amin, ya rasu a birnin tarayya Abuja.

Marigayi Idi Amin, makusanci kuma ɗan a mutun tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya rasu bayan fama da doguwar jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262