Babbar Sallah: Kiristoci Sun Taya Musulmai Sharar Masallaci A Kaduna
- Kiristoci a jihar Kaduna, sun taya Musulmai share masallacin da ake gudanar da sallolin Idi duk shekara
- Hakan ya faru ne a ƙaramar hukumar Kachia, inda kiristoci maza da mata, yara da manya suka fito don taya Musulmai nome filin sallar Idi
- Musulman sun yaba da wannan ƙoƙari da Kiristocin suka yi, inda suka yi kira da a ci gaba da zama lafiya da juna
Kachia, jihar Kaduna - A ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kaduna, mabiya addinin Kirista sun taya takwarorinsu Musulmai, sare ciyayi a ɗaya daga cikin wuraren da ake gudanar da sallar Idi a garin Kachia na jihar Kaduna.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar Musulmi ke shirye-shiryen gudanar da bukukuwan babbar Sallah.
Kiristoci maza da mata, yara da manya ne suka halarci sharar masallacin
Zargin Batanci: Gwamnatin Sokoto Ta Bayyana Irin Matakin Da Za Ta Dauka Kan Masu Batanci Ga Annabi (SAW)
Kiristoci maza da mata, yara da manya ne suka yo fitar ɗango domin taya musulmai nome ciyayin da suka mamaye filin Idin saboda yanayi na damina da ake ciki, kamar yadda Daily Trust ta yi rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen karamar hukumar Kachia, Malam Ibrahim Tasiu, ya nuna jin daɗinsa kan yadda Kiristocin suka zo don taya Musulmai share masallacin.
Ibrahim Tasiu ya yi kira ga Musulmai da Kiristoci da su ci gaba da zama lafiya da juna a faɗin jihar.
Kiristoci sun taya Musulmai murnar babbar Sallah
Haka nan kuma ya yaba wa kokarin Cibiyar Sasanci tsakanin addinai (IMC), Hukumar Zaman Lafiya ta Kaduna (KAPECOM), da Hukumar, Mercy Corps, da sauran kungiyoyin jin kai bisa irin gudummawar da suka bayar wajen tabbatuwar zaman lafiya a jihar.
Samson Auta, Ko’odinetan yanki na ƙungiyar IMC, reshen Jihar Kaduna, ya yi wa al’ummar Musulmi fatan za a gudanar da bukukuwan Sallah lafiya.
Wasu daga cikin Kiristocin da suka halarci wajen sharar, sun shaidawa Premium Times cewa wannan ba shi ne karo na farko da suka fara irin hakan ba.
Dattijo na dab da ƙwace kujerar Sanata ta Mista LA
Legit.ng ta kawo muku wani rahoto kan ɗan takarar kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya ƙarƙashin Jam'iyyar APC, Muhammad Sani Dattijo, da ya gabatar da shaidu a gaban kotu don ƙalubalantar Sanata mai ci, Lawal Adamu na PDP da ake kira Mista LA.
Hakan dai na zuwa ne bayan wasu ƙwararan shaidu da Dattijo ya gabatar a gaban kotu, waɗanda suka bayar da shaida dangane da batun karatun sanata mai ci a yanzu.
Asali: Legit.ng