Zargin Batanci: Gwamnatin Sokoto Ta Sha Alwashin Daukar Mataki Mai Tsauri Kan Masu Batanci Ga Annabi (SAW)

Zargin Batanci: Gwamnatin Sokoto Ta Sha Alwashin Daukar Mataki Mai Tsauri Kan Masu Batanci Ga Annabi (SAW)

  • Gwamnan jihar Sokoto, Dakta Ahmed Aliyu ya sha alwashin sanya kafar wando daya da duk wanda aka samu da laifin batanci ga Annabi (SAW)
  • Gwamnan ya ce ba za su zira ido a jihar kamar Sokoto, wacce mafiya yawan mazaunanta Musulmai ne, a rika yin batanci ga Ma’aiki ba
  • Gwamnan ya kuma yi kira ga mutanen jihar da su guji daukar doka da hannun, su rika kokarin sanar da hukumomi don daukar mataki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta yi hukunci mai tsauri kan duk wanda aka samu da yin batanci ga Manzon Allah (SAW).

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Abubakar Bawa ya sanyawa hannu, kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Kara karanta wannan

‘Zagin Annabi’: Shehin Malamin Musulunci Ya Yi Magana Kan Kisan da Aka Yi a Sokoto

Gwamnanatin Sokoto za ta dauki mataaki mai tsauri kan masu batanci
Gwaman Sokoto ya sha alwashin daukar mataki mai tsauri kan masu batanci ga Annabi (SAW). Hoto: Abubakar Rabi'u Dange
Asali: Facebook

Gwamnantin Sokot ta gargadi jama'a su kiaye yin kalamai na batanci

Gwamnan ya gargadi jama’a da su kiyaye aikata duk wani abu da zai iya taba darajar Ma’aiki (SAW), musamman a jaha irin Sokoto, wacce galibin al’ummarta Musulmai ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kashe wani mahauci mai suna Usman Buda, a ranar Lahadin da ta gabata bisa zarginsa da yin kalamai na batanci, kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Wasu daga cikin abokan sana’a na Buda a kasuwar da suka yi kokarin kubutar da shi sun samu raunuka, inda yanzu haka suke kwance a gadon asibiti.

Jami’an ‘yan sandan jihar sun yi alkawarin gudanar da bincike kan lamarin tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Gwamnan ya yi kira ga 'yan Sokoto su mutunta Ma'aiki (SAW)

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan da Ake Zargi Ya Sace N70bn Ya Rabawa Mutane Goron Sallar N200m

Da yake mayar da martani game da lamarin, Abubakar Bawa ya ce akwai bukatar dukkan mazauna jihar su mutunta tare da kuma kare martabar Annabi (SAW).

Sanarwar ta cewa:

“Gwamnan jihar Sokoto, Dakta Ahmed Aliyu, ya yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankula tare da bin doka da oda a kowane lokaci. Gwamnan ya ja kunnen jama’a kan duk wani abu da zai iya bata darajar Annabi Muhammad (SAW), musamman a jiha irin Sokoto, wacce Musulmi ne mafi rinjaye a cikinta.”
“Gwamna ya ce mutanen Sokoto suna mutunta Annabi Muhammad SAW sosai, don haka akwai bukatar dukkan mazauna garin su mutunta shi, su kare martabarsa da darajarsa.”
“Ina so in yi kira ga al’ummar Jihar Sokoto da su guji daukar doka a hannunsu, maimakon haka su kai rahoton duk wani laifi ko cin zarafi ga hukumomin da suka dace domin daukar matakin da ya dace.”
“Addininmu ba ya goyon bayan ɗaukar doka da hannu, saboda haka mu yi ƙoƙarin koyi da kyawawan dabi’un addininmu.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Matasa Sun Halaka Wani Mahauci A Sokoto Kan Zagin Manzon Allah

Mai magana da yawun gwamnan ya kara da cewa gwamnan ya gargadi masu son tayar da zaune tsaye da su sauya tunani, inda ya kara da cewa, ba za su samu damar yin hakan a Sokoto ba.

Ya kuma kara da cewa gwamntin jihar Sokoto ta tanaji tsattsauran hukunci ga duk wanda aka samu yana batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Farfesa Mansur Sokoto ya magantu kan abinda ya faru a jiharsa

Legit.ng ta kawo rahoto kan martanin da fitaccen malamin nan na addinin musulunci, Farfesa Mansur Sokoto ya yi bisa ga abinda ya faru a jihar tasa ta Sokoto.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da irin hakan ta taba faruwa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng