‘Yan Bindiga Sun Jawo Sarki Ya Hakura, An Dakatar da Hawan Sallah a Kasar Arewa

‘Yan Bindiga Sun Jawo Sarki Ya Hakura, An Dakatar da Hawan Sallah a Kasar Arewa

  • Mai martaba Sarkin Minna ya yanke hukunci ba za ayi hawan babbar sallah a shekarar bana ba
  • Alhaji Umar Farouk Bahago ya dakatar da hawa ne a dalilin rashin tsaro da ake kokawa da shi a Neja
  • Kimiyan Minna ya ce ba za ta yiwu a rika biki alhali ‘yan bindiga su na garkuwa da Bayin Allah ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Niger - Mai martaba Sarkin Minna, Umar Farouk Bahago, ya dakatar da yin hawan bikin babbar sallah a shekarar bana saboda matsalar rashin tsaro.

Daily Trust ta kawo rahoto a safiyar Litinin, ba za ayi hawan sallah wannan karo a Minna ba.

Alhaji Umar Farouk Bahago ya dauki wannan mataki ne domin jajantawa mutanen da aka kai wa hari musamman wadanda ke hannun ‘yan bindiga.

Hawan Sallah a Kasar Arewa
Wani Hawan Durbar a Sokoto Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

'Yan bindiga sun addabi garuruwa

Kara karanta wannan

‘Zagin Annabi’: Shehin Malamin Musulunci Ya Yi Magana Kan Kisan da Aka Yi a Sokoto

Ganin yadda mutanen garuruwan Paikoro, Munya da Shiroro su ke fama da ‘yan bindiga, Sarkin Minna ya bada umarnin fasa hawan sallah a bana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun a shekarar bara, ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da wasu manoma a karamar hukumar Paikoro, har zuwa yanzu babu labarin wadannan mutane.

Da aka zanta da shi a tashar rediyon Prestige FM, Kimiyan Minna, Alhaji Yusuf Tanko Kuta, ya tabbatar da babu maganar hawan sallah a shekarar nan.

A jawabin da ya yi a shirin “Tsalle Daya”, Yusuf Tanko Kuta ya ce Mai martaba ya dakatar da bikin ganin yadda talakawansa ke fama da ‘yan bindiga.

Jawabin Mai girma Kimiyan Minna

"Idan za ku tuna, watanni da su ka wuce migayun ‘yan bindiga su ka kai hari a Kaffin-Koro da kauyukan da ke kusa da shi, nan su ka dauke mutane.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan da Ake Zargi Ya Sace N70bn Ya Rabawa Mutane Goron Sallar N200m

Yanzu haka da mu ke magana, wadanda aka yi garkuwa da su, su na hannusu har yanzu, ba a iya kubutar da su ba.
Sannan ba da dadewa ba, wadanda su ka dauke su, su ka fitar da bidiyo da yayi yawo, Duniya ta ga yadda ake cin zarafin wadanda ba su yi laifi ba.

An rahoto Kimiyan Minna ya na cewa Mai martaba ya damu da halin mutanen nan ke ciki, saboda haka ba zai iya yin hawan sallah a irin wannan yanayi ba.

An kashe mahauci a Sokoto

Labari ya zo cewa Farfesa Mansur Sokoto ya yi magana game da kisan da aka yi a Sokoto, ya ce abin da ya faru abin takaici ne, jahilai na bukatar karatu.

Shehin musuluncin ya kara da cewa malamai na bukatar hikima wajen karantawa, sannan hukuma sai ta jajirce, a hana mutane daukar doka a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng