Tattalin Arziki: Shehu Sani Ya Bukaci Tinubu Ya Binciki Buhari, Tsoffin Ministoci Da Sauransu

Tattalin Arziki: Shehu Sani Ya Bukaci Tinubu Ya Binciki Buhari, Tsoffin Ministoci Da Sauransu

  • Sanata Shehu Sani ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya binciki laifukan tattalin arziki da aka tafka a lokacin mulkin Muhammadu Buhari
  • Tsohon dan majalisar ya ce ya kamata Tinubu ya binciki Buhari, tsoffin ministoci da shugabannin tsaro da suka yi aiki karkashin gwamnatin da ta gabata
  • Sani ya kara da cewar kada a cire tsoffin gwamnoni daga cikin wadanda za a bincika domin kada a kalli binciken da ke gudana a yanzu a matsayin son kai

Tsohon dan majalisa, Sanata Shehu Sani, ya bayyana dalilin da yasa akwai bukatar shugaban kasa Bola Tinubu ya binciki tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministocinsa da tsoffin shugabannin tsaro na gwamnatinsa.

Sani ya ce ya kamata shugaban kasa Tinubu ya binciki laifukan tattalin arziki da aka tafka a karkashin gwamnatin Buhari cike da karfin gwiwa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Wani Sojan Ruwa Ya Sharara Masa Mari a Amurka

Shehu Sani, Muhammadu Buhari da shugaban kasa Bola Tinubu
Tattalin Arziki: Shehu Sani Ya Bukaci Tinubu Ya Binciki Buhari, Tsoffin Ministoci Da Sauransu Hoto: Shehu Sani/Muhammadu Buhari/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya ce sauya fasalin naira ba shi kadai ne laifin tattalin arziki da aka aikata ba sannan kama mutum daya ko biyu ba zai samar da amsar da ake bukata ba.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter @ShehuSani, ya ce ya kamata shugaban kasa Tinubu ya fara bincike daga kan Buhari har zuwa kan na kewaye da gwamnatinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sani ya rubuta:

"Sauya fasalin naira ba shi kadai ne laifin tattalin arziki da aka tafka ba a karkashin gwamnatin Buhari. Ya kamata shugaban kasar ya yi karfin halin bayar da damar gudanar da cikakken bincike kan abubuwan da suka faru a gwamnatin Buhar, ta hanyar farawa da Buhari, tsoffin ministocinsa, shugabannin tsaronsa da na kewaye da gwamnatinsa. Haka kuma bai kamata shugaban kasar ya tsame tsoffin gwamnoni wadanda suka samu yanci yanzu, harma suke jiran samun mukaman siyasa daga wannan bincike ba. Kange mutum daya ko biyu ba zai bayar da amsa ga laifukan da sauran suka tafka ba a shekaru takwas da suka wuce. Cikin sauki za a dauki binciken da ke gudana a yanzu a matsayin na son kai idan aka takaita binciken.

Kara karanta wannan

An Shawarci Shugaban Kasa Tinubu Kan Wanda Zai Nada a Matsayin Sabon Gwamnan CBN Bayan Dakatar Da Emefiele

"Tambaya mai sauki ita ce; ya batun sauran mutane da suka bayar da gudunmawa wajen lalata tattalin arzikin? Ko kuma dai wasunmu suna da gajen hakuri ne saboda rashin masaniya kan abun da ke tunkaru mu."

Godwin Emefiele: Jigon APC ya nemi Tinubu ya binciki Sanusi

A wani labari na daban, mun ji cewa jigon APC, Kailani Muhammad, ya shawarci Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya isar da binciken da ake yi kan ofishin Godwin Emefiele har zuwa zamanin Sanusi Lamido.

Kailani ya nemi Tinubu da kada ya damu da ziyarar da tsohon sarkin Kanon ya kai masa, yana mai bayyana su a matsayin dabarun neman jan hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng