Masu POS Sun Sanar Da Sabbin Farashin Cire Kudi Da Turawa, Suna Fatan Yan Najeriya Za Su Rungumi Canjin
- Kungiyar Dillalan Bankuna ta Yanar Gizo (AMMBAN) ta sanar da sabon farashin cire kude da sakawa a wurin masu 'POS'
- Farashin zai zama gama gari a jihar Lagos don saukaka wa mutane a yanayin tattalin arziki da ake ciki
- A cewar kungiyar, sabon farashin na iya raguwa a wasu wuraren amma ba zai yi wu masu 'POS' su kara farashin ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Lagos - Kungiyar Dillalan Bankuna ta Yanar Gizo (AMMBAN) reshen jihar Lagos ta sanar da sabon farashi na masu 'POS' a jihar.
Sabon farashin an bayyana shi ne a taron shekara-shekara na kungiyar a jihar duba da matsalolin da aka fuskanta a yayin sauya fasalin Naira da kuma cire tallafin mai.
Shugaban kungiyar a jihar, Abiodun David ya ce saka sabon farashin bai rasa nasaba da yadda masu 'POS' suke karban makudan kudade tun bayan sauya fasalin Naira.
'Yan Maza Sun Kwanta: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Babban Farfesa a Najeriya Ya Koma Ga Mahaliccinsa
Ya ce duk da cewa masu 'POS' din za su iya rage farashin wanda ya danganci inda suke, amma babu hali su kara ya wuce sabon farashin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har ila yau, Sakataren kungiyar, Ogungbayi Ganiya ya ce suna kokarin sanar da Babban Bankin Najeriya (CBN) akan sabon farashin, cewar rahotanni.
Sabon farashin da kungiyar AMMBAN ta saka.
Saka kudi:
- N1,000 da N4,900 za a biya N100.
- N5,000 da N10,900 za a biya N200.
- N11,000 da N20,900 za a biya N300.
- N21,000 da N30,900 za a biya N400.
- N31,000 da N40,900 za a biya N500.
- N41,000 da N50,000 za a biya N600.
Cire kudi:
- N1,000 da N2,400 za a biya N100.
- N2,500 da N4,000 za a biya N200.
- N4,100 da N6,400, za a biya N300.
- N6,100 da N7,400 za a biya N400.
- N7,500 da N10,900 za a biya N500.
- N11,000 da N14,400, za a biya N600.
- N14,500 zuwa N17,900 za a biya N700.
- N18,000 da N20,000 za a biya N800.
Legit.ng ta bayyana yadda masu 'POS' suka rinka karbar kudaden mutane fiye da kima musamman lokacin sauya fasalin Naira a kasar.
Mutane da dama sun koka game da yadda masu 'POS' din suka kuntatawa mutane a wancan lokaci.
Tinubu Ya Ce Zai Sake Nazari Kan Tsarin Sauya Fasalin Naira da Buhari Ya Yi
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya ce zai sake nazari akan sauya fasalin Naira da tsohon shugaban kasa Buhari ya yi.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin bikin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu a Abuja.
Sauya fasalin Naira ya kawo wahalhalu ga 'yan Najeriya, inda Tinubu ya ce za a ci gaba da amfani da tsoffi da kuma sabin kudaden.
Asali: Legit.ng