“Miliyan N25 Duk Wata”: Nneka Da Wasu Jerin Mata 3 Da Suka Fi Kowace Mace Karbar Albashi Mai Tsoka a Najeriya

“Miliyan N25 Duk Wata”: Nneka Da Wasu Jerin Mata 3 Da Suka Fi Kowace Mace Karbar Albashi Mai Tsoka a Najeriya

  • Wani sabon rahoto ya bayyana sunayen manyan shugabanni mata da suka fi karbar albashi mai tsoka a fadin hukumomi daban-daban a Najeriya
  • Shugabannin da aka lissafa suna jan ragamar kamfanonin Najeriya da darajarsu a kasuwa ya yi sama da biliyan N100
  • Wadannan shugabanni mata sun kafa sunayensu a duniya kuma sun kasance madubin duba ga yan mata masu tasowa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jimillar albashin da wasu manyan mata da suka fi kowace mace daukar albashi mai tsoka ya kama miliyan N304.4 a 2022 ko miliyan N25.3 a wata. Suna jan ragamar wasu manyan kamfanonin Najeriya ne.

Wannan ya kasance ne bisa ga bayanan kudade na kamfanonin da suke jagoranta.

Oluwatomi Somefun, Owen Omogiafo, Dupe Olusola, Nneka Onyeali-Ikpe
“Miliyan N25 Duk Wata”: Nneka Da Wasu Jerin Mata 3 Da Suka Fi Kowace Mace Karbar Albashi Mai Tsoka a Najeriya Hoto: Unity bank, Fidelity, investorking
Asali: Facebook

Matan da ke karbar albashi mafi tsoka sun hada da Nneka Onyeali-Ikpe, Owen Omogiafo, Dupe Olusola, da Oluwatomi Somefun.

Kudaden da ake biyansu sun kunshi albashi, diyya da sauran alawus da ke da nasaba da mukaminsu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: A Karshe Tinubu Ya Magantu Kan Dakatar Da Emefiele, Ya Ba Da Hujja Mai Karfi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabanni mata da ke karbar albashi mafi tsoka

Ga yawan kudin da kowannensu ke karba da kuma kamfanin da suke jagoranta, kamar yadda yake kunshe a bayanan BusinessDay.

Oluwatomi Somefun- miliyan N41.7

Oluwatomi Somefun ita ce manajan daraktan bankin Unity Bank Plc. Karkashin shugabancinta, bankin ya samu gagarumin nasara duk da kalubale daban-daban.

Saboda kokarinta, ta samu jimillar diyyan naira miliyan 41.7 a 2022 kari daga miliyan N41.4 da aka rahoto a 2021.

Dupe Olusola- miliyan N62.7

Dupe Olusola ita ce manajan darakta kuma shugabar otel din Transcorp . Ita ce mace ta biyu da ke jagorantar kamfanin.

Bayanan kudin kamfanin ya nuna cewa ta samu miliyan N62.7 a 2022, kari daga miliyan N62.6 a 2021.

Owen Omogiafo- miliyan N90

Omogiafo ita ce shugabar kamfanin Transnational Corporation Plc. Ta samu naira miliyan 90 a 2022.

Kara karanta wannan

An Ba Abba Gida-Gida Wa’adin Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano, Cikakken Bayani

Nneka Onyeali-Ikpe- miliyan N110

Onyeali-Ikpe, shugabar bankin Fidelity Bank Plc ita ce ta fi kowa karbar albashi mai tsoka cikin kamfanonin Najeriya.

Ita ce a kan harkokin bankin Fidelity tun ranar 1 ga watan Janairun 2021, lokacin da ta gaji Nnamdi Okonkwo.

Saboda kokarinta a 2022, ta karbi jimillar kudi naira miliyan N110, irin wanda ta karba a 2021.

Adesina Ya Yi Alkawarin Marawa Tinubu Baya a Kokarinsa Na Karfafa Tattalin Arzikin Najeriya

A wani labari na daban, shugaban bankin raya kasashen Afrika, Akinwumi Adesina, ya yaba ma jajircewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen gina tattalin arziki mai karfi a kasar.

Adesina, wanda ya gana da shugaban kasa Tinubu yayin taron koli na kudi na duniya a birnin Paris, kasar Faransa, ya ce bankin ci gaban Afrika zai tallafawa hangen Tinubu kan tattalin arzikin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng