Dalilin Da Yasa Na Siyar Da Filin Da Ake Shirin Ruguzawa - Muhuyi Rimingado
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na Kano na ci gaba da rushe gine-ginen da tace basa bisa ka'ida a fadin jihar
- Shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafe na jihar Kano ya magantu a kan wani fili da ya siyar wanda aka yi wa alama cikin wadanda za a rushe
- Muhuyi Rimingado ya ce tun farko ya karbi filin daga gwamnatin baya ne saboda an tabbatar masa da baya da wani matsala don baya jikin makaranta, asibiti ko wurin bauta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Muhuyi Magaji Rimingado, shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafe na jihar Kano, ya yarda cewa ya siyar da wani fili cikin gine-ginen da aka yi wa alama za a rushe.
Mun dai ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi wa wasu gine-gine alama a matsayin wadanda za a rusa a jihar Kano.
Yanzu Yanzu: Abba Gida Ya Yi Makin Shaguna Da Gidajen Mai Na Miliyoyin Naira Cikin Wadanda Za a Rushe
Daga cikinsu akwai manyan shaguna da gidajen mai da ke shahararriyar hanyar BUK, da kuma wasu gine-gine da aka yi a wajajen jikin tsohuwar katangar birnin Kano wato Badala.
Isma’ila Bello, daya daga cikin mamallakan gine-ginen da ke hanyar BUK, ya bayyana cewa shugaban hukumar yaki da rashawar ne ya siyar masa da filin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dan kasuwar ya kuma zargi gwamnatin da nuna rashin adalci a shirin rusau da take yi na baya-bayan nan.
Ya yi zargin cewa wasu daga cikin gine-ginen da aka sanya cikin wadanda za a rusa an same su ne bisa ka'ida daga wuraren mutanen da ke da alaka da gwamnati mai ci.
Dalilin da yasa na siyar da filin da ake shirin rusawa, Rimingado
Sai dai Rimingado, wanda dan kasuwar ya zarga da siyar masa da filin, ya sanar da jaridar Daily Trust cewa gwamnatin baya ce ta ba shi filin kuma cewa ya karba ne saboda an tabbatar masa da cewa ba wuri ne da ya saba ka'ida ba.
Ya ce filin baya kusa da makaranta ko wurin bauta sannan bai shafi tsohuwar katangar birnin Kano ba.
Gwamnati na nuna son kai a wajen rushe-rushe, inji wani dan kasuwa
Yayin da yake jawabi ga manema labarai kan lamarin gine-ginen da gwamnatin ta sanya cikin wadanda za ta rusa a daren Juma'a, dan kasuwar, wanda ya kasance sakataren rukunin BUK Haudi Properties, ya ce ya siya filayen da suka kafa shaguna daga wajen Rimingado wanda a yanzu shi ne ke jagorantar shirin rusau din.
Bello, mazaunin unguwar Sabuwar Kofa, ya ce:
"Mun wayi gari jiya sannan muka ga zane na jan fenti a gine-ginenmu. Wannan abu da gwamnatin ke yi ba shine mafita ba. Shugaba kare rayuka da dukiyoyin mutanensa yake yi. Manyan mutane aka baiwa wurin nan a wancan lokacin.
"Lambar nasa filin (Rimingado) ya kasance 25 yana kallon Gidauniya ta wurin Hauren Shanu. Sannan idan kana maganar Badala, an gina Gidan Murtala a kan Badala sannan sauran gine-gine da ke gefen duk a Badala ne.
"Babu wani dalili na rushe-rushen kuma hankali ba zai dauka ba saboda mun same su daga gwamnatin baya sai ace a rusa."
Ya kuma yi zargin cewa akwai wasu gine-gine da ba a yi wa alamar za a rusa ba a hanyar saboda sun kasance mallakin mutane da ke kusa da gwamnati.
Martanin Rimingado
Da aka tuntube shi, Rimingado, ya ce yana nan a kan matsayinsa da ya nuna a Trust TV kan gine-ginen da aka yi wa alama don ruguzawa a Salanta sannan cewa ba daidai bane ga kowa ya yi kokarin amfani da abubuwan da ke faruwa don bata sunansa da na gwamnatin.
Ya tabbatar da cewar an ba shi fili a yankin da aka sanya cikin wadanda za a rusa amma cewa filin, wanda ya siyar a lokacin da yake bukatar kudi, baya ciki ko ba a gina shi a jikin Badala ba.
Ya ce:
"Sanya shi cikin wadanda za a rushe abu ne na daban domin dai ba cikin makaranta, wajen bauta ko asibiti yake ba. A iya sanina gwamnati na iya bayar da fili ga kowa amma gwamna ba zai iya bayar da wajen gwamnati ga kowa ba. Ina nan a kan matsayina a Trust TV.
"Ban san dalilin da yasa suka sanya wannan wuri cikin wadanda za a rusa ba. Sannan mai ginin na iya jan daaga da gwamnati don samun karin haske."
Gwamnatin Abba Gida-Gida na shirin rusa manyan shaguna da gidajen mai a Kano
A baya mun ji cewa hukumar KNUPDA ta isar da aikinta zuwa hanyar BUK daga mararrabar Dan'agundi zuwa Dukawuya ta mararrabar WTC inda aka yi makin wasu gine-gine na miliyoyin naira cikin wadanda za a rusa.
Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, ta yi makin gine-ginen da suka hada da manyan shaguna da gidajen mai na miliyoyin naira a shahararriyar hanyar nan ta BUK, cikin wadanda za a rushe.
Asali: Legit.ng