Tashin Hankali Yayin da Gwamnatin Kano Ke Shirin Rushe Manyan Shaguna Da Gidajen Mai
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da rushe gine-ginen da ya bayyana a matsayin wadanda basa bisa ka'ida a jihar
- Gwamnatin jihar Kano na shirin rushe gine-gine na miliyoyin naira da suka hada da gidajen mai da manyan shaguna a shahararriyar hanyar nan ta BUK
- Gine-ginen sun hada da SALBAS Oil and Gas Ltd, Matrix Gas Station, Matrix Petrol Station, Amna Gas Station, Double Twins Event Centre, da sauransu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Hukumar da ke da alhakin rushe-rushe ta jihar Kano ta isar da aikinta zuwa hanyar BUK daga mararrabar Dan'agundi zuwa Dukawuya ta mararrabar WTC inda aka yi makin wasu gine-gine na miliyoyin naira cikin wadanda za a rusa.
Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, ta yi makin gine-ginen da suka hada da manyan shaguna da gidajen mai na miliyoyin naira a shahararriyar hanyar nan ta BUK, cikin wadanda za a rushe.
Abba Gida-Gida na shirin rushe gine-gine mafi girma a jihar Kano, ya fadi dalili
Gine-ginen sun hada da wadanda aka gina a jikin katangar Badala wanda gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf, ya zargi magabacinsa, Abdullahi Umar Ganduje da karkatarwa ba bisa ka'ida ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa gwamnatin Abba ta kyale wasu shaguna da aka gina kan filayen da gwamnatin Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano kuma ubangidansa ya siyar.
An kammala yawancin gine-ginen da hukumar KNUPDA ta sanya cikin wadanda za a rushe yayin da yan kadan ne ake kan gina su.
Daily Trust ta rahoto cewa daya daga cikin manyan shagunan da aka kammala ya kasance mallakin gwamnatin jihar Kano ne karkashin kamfanin Kano State Investment and Properties Limited (KISP) yayin da sauran suka kasance na mutane masu zaman kansu a jihar.
An ba Abba Gida-Gida awanni 72 ya daina rushe-rushe a Kano
Legit.ng ta rahoto a baya cewa an ba gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wa'adin awanni 72 ya dakatar da aikin rushe-rushe da ke gudana a jihar da kuma hawa teburin sulhu da wadanda abun ya shafa don samun maslaha.
Kungiyar fafutukar tabbatar da makoradiyya karkashin inuwar Good Governance and Change Initiative (GGCI) ce ta bayar da wannan wa'adin.
Gamayyar kungiyar ta yi barazanar maka gwamnan a kotu idan har ya ki bin sharuddan da aka gindaya masa.
Asali: Legit.ng