Shugaba Tinubu Ya Fasa Dawowa Gida Najeriya Daga Faransa, An Bayyana Inda Jirginsa Zai Shilla

Shugaba Tinubu Ya Fasa Dawowa Gida Najeriya Daga Faransa, An Bayyana Inda Jirginsa Zai Shilla

  • A yau Asabar 24 ga watan Yunin 2023 yakamata Shugaba Tinubu ya dawo gida Najeriya daga ƙasar Faransa bayan halartar taro
  • Shugaban ƙasar ya fasa dawowa gida inda jirginsa zai shilla zuwa birnin Landan wata ziyara ta musamman ta ƙashin kansa
  • An tabbatar da cewa shugaban ƙasar zai dawo gida Najeriya akan lokaci domin riskar shagulgulan bukukuwan babbar Sallah

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda aka shirya zai dawo gida Najeriya yau Asabar daga ƙasar Faransa, zai shilla zuwa birnin Landan wata ziyara ta musamman.

Jaridar Channels tv tace hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaba Tinubu kan ayyuka na musamman, sadarwa da tsare-tsare, Dele Alake ya fitar a ranar Asabar.

Shugaba Tinubu ya fasa dawowa gida Najeriya daga Faransa
Shugaba Tinubu zai shilla birnin Landan daga Faransa Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya kammala ziyarar da ya kai a ƙasar Faransa ranar Juma'a, inda ya halarci taron da aka gudanar a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron.

Kara karanta wannan

Maciji Ya Kashe Hatsabibin Babban Kwamandan ISWAP A Dajin Sambisa

Shugaba Tinubu zai dawo kafin babbar Sallah

A cewar Alake shugaban ƙasar zai dawo Najeriya akan lokaci kafin zuwan shagulgulan bikin babbar Sallah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alake ya ƙara da cewa:

"Bayan taron da ya halarta inda ya wakilci ƙasar nan yadda ya dace, Shugaba Tinubu ya kuma yi tarurruka da manyan shugabannin ƙasashe, ƴan kasuwa da shugabannin manyan kamfanoni daga sassa daban-daban na duniya."
Shugaba Tinubu wanda a da aka shirya zai dawo birnin tarayya Abuja a ranar Asabar, yanzu zai wuce zuwa birnin Landan wata ziyara ta ƙashin kansa.

Shugaba Tinubu ya bar Najeriya ne domin zuwa birnin Faris na ƙasar Faransa a ranar Laraba, domin halartar taron da shugaba Emmanuel Macron ya jagoranta a ranar Alhamis da Juma'a.

Wannan ziyarar tasa dai ita ce ta farko zuwa ƙasar waje tun bayan da aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa na 16 a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro Ta Zo Karshe, Sabon Shugaban Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

Adesina Zai Marawa Shugaba Tinubu Baya

A wani labarin kuma, shugaban bankin raya ƙasashen Afirika, Akinwunmi Adesina ya bayyana aniyarsa ta goyon bayan Shugaba Tinubu kan manufofin da yake da su kan tattalin arziƙin ƙasar nan.

Adesina ya bayyana hakan ne a birnin Faris a ganawar da ya yi da shugaba Tinubu a birnin Faris na ƙasar Faransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng